Gwamna Ya Ɗage Dokar Zaman Gida, Ya Tabbatar da Tashin Bom Ya Halaka Mutum 16

Gwamna Ya Ɗage Dokar Zaman Gida, Ya Tabbatar da Tashin Bom Ya Halaka Mutum 16

  • Farfesa Babagana Umaru Zulum ya ɗage dokar hana zirga-zirgar da ya sanya a jihar Borno bayan tashin bom a teburin mai shayi
  • Gwamna Zulum ya kuma yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu tare da addu'ar Allah ya ba waɗanda suka jikkata lafiya
  • Babagana Zulum ya ce ƴan daba ne suka karɓe zanga-zangar da aka fara suka yi yunkurin lalata kadarorin gwamna amma Allah bai ba su nasara ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya dage dokar hana fita da ya sanya biyo bayan harin bam da aka kai a teburin mai shayi a garin Kaworu. 

Idan baku manta ba wani bom da ake zargin ƴan ta'adda suka dasa ya halaka mutum 16 a wurin mai shayi suna tsaka da fira a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Duk da barkewar rikici, gwamna ya fadi dalilin kin kulle mutane a guda

Gwamna Babagana Umaru Zulum.
Gwamna Zulum ya ɗage dokar kulle, ya yi ta'aziyyar wadanda bom ya kashe a Borno Hoto: Professor Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Meyasa Zulum ya dokar hana fita?

Wannan dalilin da kuma ɓarkewar zanga-zanga ya sa Gwamna Zulum ya ƙaƙaba dokar zaman gida a faɗin jihar domin dawo da zaman lafiya, in ji Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai a jiya Juma’a ne gwamnatin Zulum ta sassauta dokar na wani dan lokaci domin ba wa Musulmi damar gudanar da Sallar Juma’a, Channels tv ta rahoto.

Gwamna Zulum ya ɗage dokar kulle

Gwamna Zulum ya sanar da ɗage dokar na wucin gadi a wani jawabi da ya yi kai tsaye ga al'ummar jihar Borno kan halin da ake ciki.

Gwamnan ya ce ya zama dole a sanya dokar hana zirga-zirga domin daƙile yunkurin ‘yan Boko Haram na samun damar kai hare-hare kan bayin Allah.

Zulum.ya miƙa sakon ta'aziyya

Bayan haka Farfesa Zulum ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan mutum 16 da suka rasu sakamakon tashin bom a daren ranar Laraba da ta shige.

Kara karanta wannan

"Arziki da talauci duk na Allah ne," Gwamna a Arewa ya yiwa masu zanga zanga nasiha

“Ina mika ta’aziyya ga iyalan wadanda wannan mummunan lamari ya shafa da daukacin al’ummar jihar Borno. Ina kuma jajantawa wadanda suka jikkata da fatan Allah ya ba su lafiya."

Gwamna Zulum ya ce ƴan daba ne suka shiga cikin zanga-zanga, inda suka yi yunkurin lalata kayayyakin gwamnati amma jami'an tsaro suka daƙile shirinsu.

A yayin da ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, Zulum ya ce ba zai tauye haƙƙin al'umma na samar da tsaro ba.

Gwamna Namadi ya ja hankalin masu zanga-zanga

A wani rahoton na daban Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya buƙaci masu zanga-zanga su tuna cewa Allah ne kaɗai me bayarwa ko hanawa.

Gwamnan ya kuma nuna takaicinsa kan yadda ɓata gari suka yi amfani da zanga-zanga wajen satar dukiyoyin mutane a Jigawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262