Zanga Zanga: Atiku Ya Karfafi Matasa, Ya Tura Zazzafan Sako ga Tinubu

Zanga Zanga: Atiku Ya Karfafi Matasa, Ya Tura Zazzafan Sako ga Tinubu

  • Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi magana kan zanga zangar adawa da tsadar rayuwa
  • Atiku Abubakar ya ce abin a yaba ne yadda matasa suka fito suna neman kawo sauyi a harkar mulki a fadin Najeriya
  • Haka zalika Atiku Abubakar ya tura muhimmin sako ga shugaban kasa kan bukatun matasan da suka fito zanga zanga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya jinjinawa matasa kan zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Atiku Abubakar ya ce akwai matuƙar kyau yadda matasa ke maganar kawo sauyi a tsarin shugabanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Jagororin addini sun cire tsoro sun tunkari Tinubu da bukatun talakawa

Atiku da Tinubu
Atiku ya yi magana kan zanga zanga. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A cikin bayanan da ya yi a kafar Facebook, Atiku ya tura sako na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya jinjinawa matasan Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce zanga zangar da matasa suka fara ta bude sabon babi a kan shugabanci a Najeriya.

Atiku Abubakar ya yi kira ga matasan da su cigaba da yin zanga zanga lafiya da kuma kira ga wasu matasan su mara musu baya.

Zanga zanga: Sakon Atiku ga shugaba Tinubu

Atiku Abubakar ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu kan gaggauta sauraron masu zanga zangar da biya musu bukatunsu.

Ya ce lokaci ya yi da gwamnatin Bola Tinubu za ta ajiye ji da kai, ta saurari talakawan da suke zanga zanga a fadin Najeriya.

Atiku ya yi kira ga yan sanda

Kara karanta wannan

PDP ta cire adawa ta fadawa Tinubu hanyar shawo kan masu zanga zanga

Haka zalika Atiku Abubakar ya ce dole yan sanda su nuna kwarewa wajen yin aiki domin kaucewa kisa ko muzgunawa masu zanga zanga.

Har ila yau ya ce cin fuska da jami'an tsaro ke yiwa yan jarida ba abu ne da ya dace a dimokuraɗiyyance ba.

A ƙarshe ya yi kira kan kokarin ganowa da cafke masu amfani da zanga zangar wajen yin sata da tayar da tarzoma.

Zanga zanga: Wike ya fara lallaba matasa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi magana a karon farko bayan matasan Najeriya sun fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a jihohin ƙasar nan.

Ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike ne ya yi kira ga matasan Najeriya domin neman hanyar kawo karshen zanga zangar baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng