Bayan Tsohon Gwamna Ya Soki Hausa Fulani, Peter Obi Ya Wanke Kansa Daga Zagin Yan Arewa

Bayan Tsohon Gwamna Ya Soki Hausa Fulani, Peter Obi Ya Wanke Kansa Daga Zagin Yan Arewa

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi ya yi karin haske kan wani bidiyonsa da aka rika yaɗawa
  • Peter Obi ya ce an dauki nauyin wasu ne su yada bidiyon domin hada shi fada da yan Arewa da kuma gwamnatin tarayyar Najeriya
  • Jigon jami'yyar LP ya bayyana matsayarsa kan dukkan abubuwan da aka yada a cikin bidiyon da kuma kira ga gwamnatin Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT Abuja - Dan takarar jam'iyar Labour ya a zaɓen shekarar 2023 ya ya yi karin haske kan bidiyonsa da ake yaɗawa.

An yada bidiyon da aka nuna dan siyasar na magana a kan yan Arewa da kuma jogorantar zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Abuja.

Kara karanta wannan

"Jami'an tsaro sun gano sanata mai daukar nauyin zanga zanga," Minista Wike ya yi magana

Peter Obi
Obi ya wanke kansa kan bidiyon yaki da Arewa. Hoto: @PeterObi
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da Peter Obi ya yi ne a cikin wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Ban zagi Arewa ba' Inji Peter Obi

Peter Obi ya bayyana cewa an saka bidiyonsa da ya yi magana a wani taro a jihar Anambara da aka juya cewa yana fada ne da Arewa.

Sai dai ya bayyana cewa a lokacin taron ya yi magana ne kan yaki da cin hanci da rashawa, ci bayan tattalin arziki da rashin tsaro.

Peter Obi ya jagoranci zanga zanga?

Haka zalika Obi ya ce an wallafa bidiyonsa da aka juya cewa shi ne yake jagorantar zanga zanga a garin Abuja.

Peter Obi ya bayyana cewa bai jagoranci zanga zanga ba, bidiyon kuma an dauke shi ne wata rana da yaje ofishin jami'yyar LP a Abuja.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi magana kan zanga zanga, ya fadi hassadar da ake yi wa jihar Kano

Obi kan 'korar' yan ƙabilar Ibo

A karshe Peter Obi ya yi martani kan maganar da ake yaɗawa ta korar yan ƙabilar Ibo daga jihar Legas zuwa jihohinsu.

Ya ce hakan ya saɓa dokar kasa kuma ya kamata jami'an tsaro su gaggauta daukan matakin a kan lamarin.

Tsohon gwamna ya caccaki yan Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa Ayodele Fayose ya soki wasu ƴan Arewa da suke yawan haihuwa ba tare da samun isassun kudin kulawa da ƴaƴansu ba.

Tsohon gwamnan jihar Ekiti ya bayyana cewa hakan karawa gwamnati nauyi ne wadda a yanzu take kokarin tsayawa da kafafunta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng