Bidiyo: Kiristoci Sun Ba Musulmai Masu Sallar Juma’a Kariya Ana Tsaka da Zanga Zanga

Bidiyo: Kiristoci Sun Ba Musulmai Masu Sallar Juma’a Kariya Ana Tsaka da Zanga Zanga

  • An ga Kiristoci su na ba Musulmai kariya a lokacin da suka gabatar da Sallar Juma'a ana tsada da zanga-zanar yunwa a garin Osogbo
  • A cikin bidiyon wanda aka nade shi a rana ta biyu ta zanga-zangar, an ga hadin kai da kuma kaunar juna tsakanin mabiya addinan
  • Wannan abu da ya faru ya nuna cewa zanga-zangar ta kara fito da hadin kan 'yan kasar a fili duk da cewa ta gamu da tashe tashen hankula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osogbo, Osun - A wani abu da ya nuna kaunar juna tsakanin addinai, an ga Kiristocin garin Osogbo suna ba da kariya ga Musumai yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a fadin kasar.

Kara karanta wannan

An shiga rana ta 2 na zanga zanga, jama'a sun fara hallara a garin Tinubu

Kamar yadda aka gani a wani bidiyo da aka nada a rana ta biyu ta zanga-zangar, Musumai ne ke gabatar da Sallar Juma'a yayin da ake zanga-zangar adawa da yunwa da tsadar rayuwa.

Kiristocin Osogbo sun ba Musulmi kariya lokacin da suke Sallah ana tsaka da zanga-zanga
Zanga-zanga: An ga Kiristoci suna kare Musulmi lokacin Sallah. Hoto: @Olamide0fficial
Asali: Twitter

Osun: Kiristoci sun ba Musulmi kariya

Jaridar Daily Trust ce ta wallafa bidiyon lokacin da Kiristoci ke gadin Musulman a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zangar wacce aka fara tun ranar 1 ga Agusta, 2024, ta tara kungiyoyi daban-daban wadanda ke nuna goyon baya ga juna.

Duk da cewa zanga-zangar ta gamu da tashe tashen hankula a sassa daban daban na kasar, sai dai abin da ya faru a Osogbo ya kara nuna cewa mabiya addinai a Najeriya na kaunar juna.

Kalli bidiyon a kasa:

Mutane sun yi martani kan bidiyon

Legit Hausa ta tattaro martanin mutane kan wannan bidiyo da ya yadu.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Yan sandan Kano sun kara himma, an kara cafke masu cin 'ganima'

@Nairaexchanger:

"Yan Najeriya na kaunar juna kawai dai matsalar na daga shugabanni da kuma wasu ba ta gari da ke son haddasa fitina a kullum."

@HRH_bankeoniru:

"Irin hakan ma ta taba faruwa a lokacin zanga-zangar #EndSARS"

@premier_king001:

"Ubangiji ya kara hada kanmu."

@Sirjigo:

"Yan Najeriya 'yan uwan juna ne kawai dai 'yan siyasa ne suka kawo rabuwar kai domin cimma wata manufa tasu."

Kano: An sassauta dokar hana fita

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta sassauta dokar hana fita saboda ba al'ummar Musulmi damar zuwa masallacin Juma'a.

Gwamnatin ta ce ta sassauta dokar daga karfe 12:00 na rana zuwa karfe 5:00 na yamma inda daga nan ne kuma dokar za ta ci gaba da aiki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.