Bayan Gwamna a Arewa Ya Ki Albashin N70,000, NLC Ta Fadi Matakin da Za Ta Dauka

Bayan Gwamna a Arewa Ya Ki Albashin N70,000, NLC Ta Fadi Matakin da Za Ta Dauka

  • Kungiyar Kwadago ta NLC a jihar Gombe ta caccaki Gwamna Inuwa Yahaya na jihar kan biyan mafi karancin albashin N70,000
  • Sakataren kungiyar, Ibrahim Fika ya tabbatar da haka inda ya ce za su saka kafar wanda daya da gwamnan kan hakkin ma'aikata
  • Legit Hausa ta yi magana da wani ma'aikacin gwamnatin jihar a Gombe kan martanin NLC game da bayanan Gwamna Inuwa.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Kungiyar kwadago reshen jihar Gombe ta yi barazanar saka kafar wando daya da Gwamna Inuwa Yahaya.

Kungiyar ta bayyana haka bayan gwamnan ya tabbatar da cewa ba zai iya biyan mafi karancin albashin N70,000 ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gama shiri, zai fara biyan ma'aikata sabon albashi ana tsaka da zanga zanga

NLC ta caccaki gwamna kan kin amincewa da mafi karancin albashi
Kungiyar NLC ta ce za ta dauki mataki kan Gwamna Inuwa game da albashin N70,000. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Asali: Facebook

NLC ta fusata game da kalaman Inuwa

Sakataren NLC a jihar, Ibrahim Fika ya fadawa wakilin Punch cewa hakan ya tabbatar musu da cigaba da gwagwarmaya a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fika ya ce gwamnan ya fadi abin da ke ransa, muna sauraron umarni daga hedikwatar kungiya saboda cigaba da gwagwarmaya.

Ya ce maganar karin albashi a yanzu ta zama doka saboda Shugaba a Bola Tinubu ya sanya mata hannu bayan amincewar majalisa, a cewar Daily Post.

Matakin NLC kan Gwamna Inuwa a Gombe

"Gwamnan ya fadi abin da yake ransa, za mu cigaba da gwagwarmaya saboda abin da muka sani shi ne karin albashi ya zama doka a yanzu."
"Babu wani dalili da gwamnan zai ce ba zai iya biyan mafi karancin albashin N70,000 ba, ba mu tsammanin su biya fiye da haka kuma ban da kasa da haka."

Kara karanta wannan

Karin albashi: Gwamnatin Tinubu ta karo kudin shiga, Gwamna ya fadi matsalar da aka fada

"Za mu yi duka kokarinmu wurin tabbatar da cewa ma'aikatan jihar Gombe sun samu mafi karancin albashin N70,000."

- Ibrahim Fika

Legit Hausa ta yi magana da wani ma'aikacin gwamnatin jihar a Gombe kan martanin NLC game da bayanan Gwamna Inuwa.

Abubakar Sadik Abdulkadir da ya bukaci boye ma'aikatarsa ya ce gaskiya dai ya kamata kungiyar NLC ta dauki matakin da ya dace.

"Dole sai sun yi da gaske kafin tilasta wannan gwamna na mu saboda ma'aikata na kuka da shi."
"Kamar yadda wasu ke kira ne ya kamata duk gwamnan da ya fandare kan wannan karin albashi ya yi murabus."

- Sadik Abdulkadir

Gwamna ya ce albashin N70,000 da yawa

Kun ji cewa gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya ce ba zai iya biyan albashin N70,000 ba a matsayin mafi karanci.

Inuwa ya bayyana cewa da kyar yake iya biyan N30,000 din ma a halin da ake ciki na rashin kudi bare kuma har N70,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.