Zanga Zanga: Jagororin Addini Sun Cire Tsoro Sun Tunkari Tinubu da Bukatun Talakawa

Zanga Zanga: Jagororin Addini Sun Cire Tsoro Sun Tunkari Tinubu da Bukatun Talakawa

  • Kungiyar hadin kan addinai a Najeriya ta yi kira na musamman ga yan kasa da shugaba Bola Ahmed Tinubu kan zanga zanga
  • Mai alfarma Sarkin Musulmi da shugaban kungiyar CAN ne suka amince da sanarwar da kungiyar ta fitar a yau Jumu'a
  • Kungiyar ta yi kira ga matasa da sauran jami'an tsaro kan yadda za a samar da zaman lafiya mai dorewa a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyar hadin kan addinai a Najeriya (NIREC) ta yi kira kan kawo karshen zanga zanga a Najeriya.

Kungiyar NIREC ta yi kiran ne ga shugaban kasa Bola Tinubu da matasa domin kaucewa tashin fitina a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: CUPP ta bayyana babban kuskuren da zai iya jefa Tinubu a matsala

Zanga zanga
Kungiyar NIREC ta yi kira ga Tinubu kan zanga zanga. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar da shugaban kungiyar CAN ne suka yi kiran.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga zanga: Kiran Kungiyar NIREC ga Tinubu

Kungiyar NIREC ta bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta gaggauta biyan bukatun yan Najeriya da ke zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Sakataren kungiyar NIREC, Farfesa Cornelius Afebu Omonokhua ne ya rattaba hannu kan takardar da kungiyar ta fitar a yau Juma'a.

NIREC ga matasa: 'Ku ajiye zanga zanga'

Vanguard ta wallafa cewa NIREC ta ce lallai akwai wahalar rayuwa a Najeriya kuma matasa suna kan gaskiya wajen nuna damuwa.

Sai dai duk da haka kungiyar ta yi kira ga matasa kan dakatar da zanga zangar saboda yadda lamarin ke kara rikicewa a Najeriya.

NIREC ta yi kira ga jami'an tsaro

Haka zalika kungiyar NIREC ta bukaci jami'an tsaro da su nuna kwarewa a yayin aikin samar da zaman lafiya a lokacin zanga zanga.

Kara karanta wannan

PDP ta cire adawa ta fadawa Tinubu hanyar shawo kan masu zanga zanga

Kungiyar ta ce babbar bukatar ta ita ce samar da kasa mai zaman lafiya da kowa zai yi alfahari da ita.

Zanga zanga ta jawo asara a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa zanga zangar da matasa suka fara gudanarwa a Najeriya kan tsadar rayuwa ta jawo asarar rayuka da dukiya mai dimbin yawa.

An ruwaito cewa an kashe mutane da dama a jihohin Kaduna, Borno, Neja da sauransu ciki har da jami'an tsaro yayin zanga zangar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng