Kano: 'Yan Sanda Sun Saki Bidiyon Masu Zanga Zanga Suna Wawushe Dukiyar Jama’a

Kano: 'Yan Sanda Sun Saki Bidiyon Masu Zanga Zanga Suna Wawushe Dukiyar Jama’a

  • Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Olumuyiwa Adejobi ya saki bidiyon yadda wasu masu zanga-zanga ne ke satar dukiyar jama'a
  • A cewar Olumuyiwa Adejobi matasan sun saci kayayyakin ne a jihar Kano a ranar Alhamis bayan barkewar zanga-zangar yunwa
  • Hakazalika, kakin rundunar ya saki hotunan wasu daga cikin kayayyakin sata da ya ce 'yan sanda sun kwato a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kwato dukiyar jama'a da ake zargin masu zanga-zanga sun wawure a jihar.

An ce wasu 'yan daba ne suka saje da masu zanga-zangar lumana a jihar inda suka rika balle shagunan jama'a suna kwasar kayansu.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan sanda na kokarin kakkabe miyagu, an kama 'yan daba 50 a Katsina

'Yan sanda sun yi magana kan masu fakewa da zanga-zanga suna satar dukiyar jama'a a Kano
Kano: 'Yan sanda sun saki hotuna da bidiyon yadda masu zanga-zanga suka saci dukiyar jama'a. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Olumuyiwa Adejobi ya sanar da hakan a shafinsa na X a ranar Juma'a, 2 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama kayayyakin sata a Kano

Sanarwar ta ce:

"Wadannan su ne kadan daga cikin kayayyakin da aka kwato daga masu zanga-zanga. Yanzu haka an jazawa masu dukiyar nan asara mai yawa.
"Wadanda aka yi wa satar nan 'yan uwa ne da abokan arziki wadanda ke fafutukar daukar dawainiyar rayuwarsu. Yanzu wannan za mu kira zanga-zangar lumana?"

Kamar yadda hotunan da kakin 'yan sandan ya wallafa suka nuna, an kama kayayyakin da suka hada da jarakunan mai, katifa, kayan abinci, batirin inbata da dai sauransu.

Kalli hotunan a kasa:

Bidiyon masu zanga-zanga na sata

A wani faifan bidiyo da kakakin rundunar 'yan sandan ya wallafa a shafinsa na X, an ga yadda wasu masu zanga-zanga, musamman matasa suna jidon kayayyaki a kansu.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Yan sandan Kano sun kara himma, an kara cafke masu cin 'ganima'

Olumuyiwa Adejobi ya yi ikirarin cewa wadannan kayayyakin da masu zanga-zangar ke jidowa kayan sata ne ba wai nasu ba.

A cewar Olumuyiwa Adejobi:

"Masu zanga-zanga na satar dukiyar jama'a a Kano a ranar Alhamis.... Har yanzu kuna kallon wannan a matsayin zanga-zangar lumana?"

Kalli bidiyon a kasa:

Jigawa: An kona hedikwatar APC a zanga-zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa an kona hedikwatar jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa bayan da zanga-zangar lumana ta koma tashin hankali.

Rahotanni sun cewa sai da masu zanga-zangar suka fara sace kayayyakin ciki kafin suka kona ginin ofishin da motocin da aka ajiye a harabar wurin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.