Nasarawa: Ciyaman Ya Dauki Mataki Kan Masu Zanga Zanga, ’Yan Daba Sun Yi Barna

Nasarawa: Ciyaman Ya Dauki Mataki Kan Masu Zanga Zanga, ’Yan Daba Sun Yi Barna

  • Shugaban karamar hukumar Karu, James Thomas ya sanya dokar hana fita ta awanni 12 sakamakon zanga-zanga
  • Wannan na zuwa ne yayin da aka samu bullar rahoton tashin hankula a wasu sassa na karamar hukumar a safiyar yau
  • Karamar hukumar Karu na makwaftaka da babban birnin tarayya Abuja kuma nan ma an gudanar da zanga-zangar yunwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Jihohi musamman na Arewa na ci gaba da daukar matakai yayin da zanga-zangar lumana ta rikide zuwa ta tashin hankali a sassan kasar.

A yayin da wasu gwamnoni suka ayyana dokar hana fita ta awanni 24, wasu jihohin kuma an haramta zanga-zangar gaba daya.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sanda sun saki bidiyon masu zanga zanga suna wawushe dukiyar jama'a

Shugaban karamar hukuma a Nasarawa ya sanya dokar hana fita saboda zanga-zanga
Nasarawa: An sanya dokar hana fita a karamar hukumar Karu saboda zanga-zanga. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

TVC News ta ruwaito cewa an sanya dokar hana fita daga faduwar rana zuwa wayewar gari a karamar hukumar Karu da ke jihar Nasarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sanya dokar hana fita a Karu

Karamar hukumar Karu na makwaftaka da babban birnin tarayya Abuja kuma an samu rahotannin tashin hankula daga yankin a safiyar yau.

Shugaban karamar hukumar, James Thomas ne ya sanar da sanya dokar a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

Mai taimakawa shugaban karamar hukumar Karu ta fuskar yada labarai Danbaba Magaji ne ya fitar da sanarwa a ranar Alhamis, inji rahoton Channels TV.

Dalilin sanya dokar hana fita a Karu

Sanarwar ta ce an sanya dokar ne a kan mutane, ababen hawa daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na Asubah.

A cewar sanarwar:

“Shugaban karamar hukumar Karu, James Thomas, ya sanya dokar hana fita a fadin Karu daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe daga yau har zuwa wani lokaci.”

Kara karanta wannan

Wani gwamnan Arewa ya sake hana zanga zanga, an sanya dokar awa 24 babu fita

Da take ba da dalilin sanya dokar hana fitan, karamar hukumar ta ce "an sanya dokar ne a matsayin matakin riga-kafi domin tabbatar da cikakken tsaro a Karu."

Zanga-zanga: An sanya doka a jihohin 4

A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla jihohi hudu na Arewa ne aka sanya dokar hana fita ta awanni 24 biyo bayan tashin hankula da aka samu a yayin zanga-zanga a jiya Alhamis.

Gwamnonin jihohin Kano, Katsina, Jigawa, Yobe da kuma Borno (inda aka sanya dokar saboda tashin bam) sun dauki matakan ne domin kare dukiyoyi da rayukan al'ummarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.