Zanga Zanga: Yan Sandan Kano Sun Bada Himma, An Kara Cafke Masu Cin 'Ganima'

Zanga Zanga: Yan Sandan Kano Sun Bada Himma, An Kara Cafke Masu Cin 'Ganima'

  • Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana karin nasara a kan bata-garin da suka saci kayan jama'a yayin zanga-zanga a ranar farko
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kamen bayan jami'an tsaro sun ci gaba da aikinsu
  • Kamen na zuwa ne bayan matasan da su ka fito zanga-zanga su ka hadu da 'yan daba ana yashe wasu shaguna da aka fasa a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana karuwar wadanda ake zargi da fasa shagunan jama'a da kadarorin gwamnati tare da yi masu wasoso.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Kiristoci sun ba Musulmai masu sallar Juma'a kariya ana tsaka da zanga zanga

A ranar 1 Agusta, 2024 da aka fara zanga-zanga ne aka samu akasi ta rikide daga ta lumana zuwa sata da tashe-tashen hankula.

Jihar
Yan sanda sun kara kama masu sata yayin zanga-zanga Hoto: SP Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Jami'in hulda da jama'a na rundunar ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa yanzu an kama mutane 269.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: Yan sanda sun kwato kayayyaki

Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana takaicin yadda zanga-zanga ta rikide zuwa sace-sace da kone-kone a fadin jihar.

Jaridar Daily trust ta wallafa rundunar ta kwato wasu daga cikin kayan da aka sace; jarkoki 25 na man gyada da sauran kayan abinci.

A ranar Alhamis dai an fasa hukumomin gwamnati da gidajen mai da daidaikun dakunan adana kayayyaki a jihar

"Za a hukunta masu tada tarzoma," Yan sanda

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Kano, SP Kiyawa ya ce yanzu haka wadanda aka kama su na sashen binciken manyan laifuka na rundunar.

Kara karanta wannan

Jama'a sun yi kunnen ƙashi, an fito zanga zanga a rana ta 2 duk da dokar hana fita

Ya ce ba za su saurarawa duk wanda aka kama da kokarin tayar da zaune tsaye a fadin jihar ba.

Masu zanga-zanga sun yi ta'adi

A baya mun ruwaito cewa matasa ciki har da masu karancin shekaru ne su ka fito zanga-zanga a jihar Kano yayin da aka fara zanga-zangar gama gari.

Jama'a sun shiga firgici bayan zanga-zangar ta rikice zuwa sata, inda aka gano yara ƙanana su na dibar kayayyaki daga cikin shagunan jama'a da sunan ganima.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.