Masu Zanga Zanga Sun Kona Ofishin 'Yan Sandan Abuja? An Samu Cikakken Bayani

Masu Zanga Zanga Sun Kona Ofishin 'Yan Sandan Abuja? An Samu Cikakken Bayani

  • Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja ta musanta ikirarin cewa masu zanga zanga sun kona ofishin dakarun a Nyanya
  • SP Josephine Adeh, kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, ta ce wani dakin kwantena da ke a ofishin ne kawai aka farmaka
  • Jami'ar tsaron ta kara da cewa an kama wasu mutane hudu a lokacin da suke kokarin kai hari ofishin ‘yan sanda na Tipper Garage

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rundunar ‘yan sandan Abuja ta musanta rahotan cewa masu zanga-zanga sun kona ofishin ‘yan sanda na Nyanya a ranar Alhamis 1 ga watan Agusta.

A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan, SP Josephine Adeh, an kai harin ne kan wani dakin kwantena na 'yan sandan da ke bincike a Nyanya, ba babban ofishin yankin ba.

Kara karanta wannan

"An kashe dan sanda": IGP ya ba jami'an tsaro sabon umarni kan masu zanga zanga

Rundunar ‘yan sandan Abuja ta musanta rahoton da ke cewa an kai hari ofishin ‘yan sanda na Nyanya
‘Yan sanda sun musanta harin da aka kai ofishin ‘yan sandan Nyanya da ke Abuja. Hoto: @aonanuga1956, @PoliceNG
Asali: Twitter

An kama masu zanga-zanga a Abuja

SP Adeh ta fayyace cewa an kona dakin kwantena na jami'an, amma babu abin da ya samu babban ofishin 'yan sandan yankin, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kuma bayar da rahoton wani yunkurin lalata ofishin ‘yan sanda na Tipper Garage da wasu mutane hudu da ake zargi suka yi, wadanda aka yi nasarar kama su.

SP Adeh ta bayyana sunayensu kamar haka: Mathias Jude, Mohammad Ahmed, Abba Jibril, da Mohammad Haruna.

'Yan sanda sun gargadi masu zanga-zanga

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igweh, ya amince da ‘yancin gudanar da zanga-zanga amma ya yi Allah wadai da barnata dukiyar jama’a.

Jaridar Vanguard ta ruwaito CP Benneth Igweh ya yi gargadin cewa masu zanga-zangar da aka kama da laifin lalata dukiya za su fuskanci cikakken fushin hukuma.

Kara karanta wannan

"Jami'an tsaro sun gano sanata mai daukar nauyin zanga zanga," Minista Wike ya yi magana

'Yan sanda na daukar matsaya mai tsauri kan tashin hankali da barna a lokacin zanga-zanga yayin da suke amincewa da 'yancin gudanar da zanga-zangar lumana.

IGP ya ba 'yan sanda sabon umarni

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sufeta Janar, Kayode Egbetokun ya umarci ƴan sanda su ɗauki mataki mai tsauri kan duk wanda suka kama da laifi a faɗin kasar nan.

IGP Egbetokun ya bayar da wannan umarnin ne a lokacin da yake nuna takaicin yadda masu zanga-zanga suka kashe jami'in dan sanda guda da lalata ofisoshin rundunar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.