Zanga Zanga: Yadda Yara Su Ka Rika Sata a Kano Ya Tsorata Jama'a
- Masu amfani da shafukan sada zumunta sun shiga zullumi bayan ganin yara kanana su na satar jarkokin man gyada
- Dan jaridar da ya dauki rahoton da ya karade shafukan sada zumunta ya shaidawa Legit cewa gidan adana kayan Barakat store aka fasa
- Daruruwan matasa ne su ka rika daukar jarkokin mai a kawunansu su na fadin ai hakkinsu su ka dauka daga mahukunta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - An tafka ta'asa yayin gudanar da zanga-zanga a ranar farko a birnin Kano da kewaye inda jama'ar gari da 'yan daba su ka rika satar kayan jama'a.
Abin da ya fi daukar hankalin jama'a shi ne yadda yara kanana su ka rika satar jarkokin mai ba tare da nuna tsoro ba
A wani sakon Facebook da Muhammad Aminu Kabir ya wallafa, kuma mai ba wa gwamnan Kano shawara a kan jin kai, Fauziyya D Sulaiman ta sake wallafawa, an gano matasan su na gudu da jarkokin mai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga-zanga: Matasa sun dauki makami ana zage-zage
Yayin da matasan Kano su ka rika satar jarkokin man gyada a kawunansu su ma tafiya da shi gida, an hango wasu daga cikinsu rike da adda.
Matasan sun rika zage-zage su na fadin ai hakkinsu ne aka rufe a dakin adana kaya, saboda haka sun ci ganima kawai.
An fasa shago da sunan zanga-zanga
Da Legit ta tuntubi Mukhtar Yahya Usman da ya dauki bidiyon matasan, ya ce ba zai iya lissafa jarkokin mai da talabijin da wasu kayayyaki da aka sata ba.
Mukhtar Yahya Usman ya kara da cewa shagon adana kayan wani shagon sayar da kayan masarufi na Barakat masu zanga-zangar su ka fasa.
Gwamnan Kano ya sanya doka saboda zanga-zanga
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana zirga-zirga ta awanni 24 biyo bayan tashin hankali da ya jawo asarar rai
Yau ce ranar farko da jama'a su ka fito tituna domin nuna adawa da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, amma lamarin ya koma tashin hankali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng