An Shiga Tashin Hankali a Borno Yayin da Aka Kashe Matasa 4 Ana Tsaka da Zanga Zanga

An Shiga Tashin Hankali a Borno Yayin da Aka Kashe Matasa 4 Ana Tsaka da Zanga Zanga

  • Matasa hudu da ake zargin ma’aikata ne sun mutu a wani gidan mai na Kime da ke kwanar Bolori a babban birnin jihar Borno
  • Duk da cewa babu wani rahoto da ya bayyana taka maimai abin da ya kashe matasan, wata majiya ta ce harbin bindiga ne
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar Borno ta sanya dokar hana fita ta awanni 24 bayan fashewar bam a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Yayin da zanga-zanga ta rikide zuwa tashin hankali, an kashe wasu matasa hudu a gidan man Kime da ke kwanar Bolori a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Jami’an gidan man da suka bayyana matasan a matsayin ma’aikatansu, sun yi sabani a bayanin yadda suka mutu.

Kara karanta wannan

"Jami'an tsaro sun gano sanata mai daukar nauyin zanga zanga," Minista Wike ya yi magana

An kashe matasa hudu ana tsaka da zanga-zanga a Borno.
Borno: An kashe matasa hudu a wani gidan mai ana tsaka da zanga-zanga. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An kashe matasa 4 a jihar Borno

"Ko a yanzu da nake magana da ku, gawarsu na can kwance a cikin jini."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Inji daya daga cikin ma'aikatan da ya bayyanawa jaridar Daily Trust sunansa Malam Musa.

Malam Musa wanda ya tabbatar da cewa yana tare da matasan a lokacin da abin ya faru da su ya ce sun mutu ne sakamakon fashewar wani abu.

"Ni ma Allah ne ya tseratar da ni na tsallake rijiya ta baya, na tsira ba tare da jin rauni ba."

- A cewar Malam Musa.

"Harsashin bindiga ya kashe matasan" - Majiya

Sai dai jaridar Vanguard ta ruwaito wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta ce harsashin bindiga ne ya kashe matasan.

“Ina daura da gidan man ne lokacin da lamarin ya faru, babu wani abu kamar fashewar bam, kawai mun ji karar harbe-harbe sai yaran suka fadi."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Masu zanga zanga sun cinnawa hedikwatar APC wuta, bayanai sun fito

A wani rahoton kuma, an tattaro cewa babu alamar harsashi/harbin bindiga a jikin wadanda abin ya shafa.

Zulum ya sanya dokar hana fita a Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar ‘yan sanda ta sanar da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a jihar Borno, saboda rikicin da ya barke a zanga-zangar da aka yi a fadin kasar.

Rundunar ta ce ta sanya dokar ne bisa umarnin Gwamna Babagana Zulum wanda ya gana da jami'an tsaro bayan harin Bam da ya auku a kauyen Kawuri da ke Konduga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.