Zanga Zanga: Matasa Sun Cinnawa Sakatariya Wuta, ’Yan Sanda Sun Dauki Mataki

Zanga Zanga: Matasa Sun Cinnawa Sakatariya Wuta, ’Yan Sanda Sun Dauki Mataki

  • Wasu matasa sun yi amfani da zanga-zanga inda suka banka wuta a wani bangare na sakatariyar karamar hukuma a Niger
  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kama wasu mutane 11 da ake zargi da hannu a saka wutar a sakatariyar karamar hukumar Tafa
  • Hakan na zuwa bayan barkewar zanga-zanga a fadin kasar baki daya saboda halin kuci da matsanancin 'yunwa da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - Rundunar 'yan sanda a jihar Niger ta cafke wasu matasa da ake zargin sun cinnawa sakatariyar karamar hukumar Tafa wuta.

Rundunar ta tabbatar da kama mutane har guda 11 yayin zanga-zanga a jihar wacce ta rikide kamar sauran jihohin Arewa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Masu zanga zanga sun cinnawa hedikwatar APC wuta, bayanai sun fito

'Yan sanda sun kama matasa 11 a Niger yayin zanga-zanga
An kama wasu matasa yayn zanga-zanga da zargin kona sakatariyar karamar hukuma. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun shi ya bayyana haka a yau Alhamis 1 ga watan Agustan 2024, cewar Vanguard.

Abiodun ya ce matasan sun kuma cinnawa wasu motoci biyu wuta tare da lalata wasu biyu bayan sace-sace a wurin.

Ya ce abin takaici ne yadda wasu suka yi amfani da zanga-zangar suka tafka barna tare da sace-sace da lalata dukiyoyin al'umma, ThisDay ta tattaro.

"Wasu miyagu daga Tafa a karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna da wasu a karamar hukumar Gurara a Niger sun farmaki sakatariyar karamar hukumar Tafa a jihar Niger."
"Maharan sun tafka barna a sakatariyar da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka cinnawa wasu motoci wuta da lalata wasu."
"Matasan sun cinnawa wani bangare na sakatariyar wuta tare da lalata kaya da kuma sace-sace."

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa da aka sanya dokar hana fita ta awa 24 sun kai 4, an samu cikakken bayani

- Wasiu Abiodun

'Yan sanda sun gargadi iyaye a Niger

Abiodun ya ce jami'an tsaro sun tarwatsa matasan da suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja yayin da yanzu aka bude hanyar ga masu ababan hawa.

Rundunar ta gargadi iyayen yara da su gargadi 'ya'yansu inda ta ce ba za ta daga kafa ga duk wadanda aka same su da ta da tarzoma ba.

Kotu ta dakile masu zanga-zanga

A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun jihar Ogun ta yi hukunci kan korafin da aka shigar kan masu shirin zanga-zanga.

Kotun ta umarci masu zanga-zangar da su gudanar da shirin na su a wurare guda hudu kacal a fadin jihar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.