Bidiyo: Masu Zanga Zanga Sun Cinnawa Hedikwatar APC Wuta, Bayanai Sun Fito

Bidiyo: Masu Zanga Zanga Sun Cinnawa Hedikwatar APC Wuta, Bayanai Sun Fito

  • Rahotanni sun nuna cewa fusatattun matasa daga cikin masu zanga-zanga sun kona ofishin jam'iyyar APC a jihar Jigawa
  • An ce matasan sun fara lalata alluna da kayayyakin sanarwa na jam'iyyar kafin suka kona ofishin da motocin da ke ciki
  • A Birnin Kudu inda wasu suka samu raunuka, an ce 'yan barandan sun fasa shagunan taki da hatsi suka tafka sata a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jigawa - Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa hedikwatar jam’iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa na cin wuta.

An tattaro cewa an kona sakatariyar ne a lokacin rikici ya barke a zanga-zangar adawa da yunwa da aka fara yi a fadin kasar.

Kara karanta wannan

"An kashe dan sanda": IGP ya ba jami'an tsaro sabon umarni kan masu zanga zanga

Fusatattun matasa sun kona ofishin jam'iyyar APC na Jigawwa
Jigawa: Masu zanga-zanga sun kona ofishin APC, sun kwashe kayayyaki. Hoto: @moore_ojo
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu fusatattun matasa ne suka farmaki ofishin da ke Dutse babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kona ofishin APC a zanga-zanga

An ce matasan sun fara lalata alluna da sauran kayayyakin sanarwar jam'iyyar kafin suka kutsa kai ciki tare da cinnawa ofishin wuta.

Sun kuma kona motocin da aka ajiye a cikin harabar ofishin jam'iyyar, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Rikicin ya yadu zuwa wasu sassan jihar yayin da matasan da ke dauke da makamai suka rika ta'adi duk da kokarin da jami’an tsaro ke yi na dakile su.

Masu zanga-zanga sun lalata dukiya

A Birnin Kudu inda wasu suka samu raunuka, an ce 'yan barandan sun fasa shagunan sayar da taki da hatsi na jihar inda suka kwashi na kwasa.

An ce 'yan daban sun kuma kai hari a kamfanin sayar da kayan gona na jihar (JASCO) da ke Gumel inda nan ma suka lalata shi tare da sace kayayyaki.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Borno yayin da aka kashe matasa 4 ana tsaka da zanga zanga

‘Yan ta’addan sun kuma kai hari gidan dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabun Gumel, Gagarawa da Maigatari a birnin Abuja.

Ana zargin an kai gari har gidan mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar duk a Jigawa.

Kalli bidiyon a kasa:

An sanya dokar hana fita a Yobe

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Mai Mala Buni ya sanya dokar hana fita ta awanni 24 a jihar Yobe bayan barkewar rigima sakamakon zanga-zangar da ake yi.

Gwamnatin jihar ta ce ta gano shirin wasu 'yan ta'adda na sajewa da masu zanga-zangar domin lalata kadarorin gwamnati da sace dukiyar jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.