An Shiga Fargaba Daga Zanga Zanga, 'Yan Daba sun Fara Kwace Iko da Titin Abuja

An Shiga Fargaba Daga Zanga Zanga, 'Yan Daba sun Fara Kwace Iko da Titin Abuja

  • An shiga fargaba a yankin Kubwa da ke babban birnin tarayya Abuja bayan 'yan daba sun karbe zanga-zanga daga hannun yan gari
  • Tuni 'yan daban su ka fara karbar kudi daga hannun masu zirga-zirga a hanyar, lamarin da ya kara firgita jama'a
  • Ana ganin 'yan daban da ke karbar kudaden daga jama'a sun fi 100 inda su ka rufe hanyoyi tare da kona taya a tituna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Mazauna Abuja, musamman wadanda ke yankin Kubwa sun shiga rudani bayan yan daban sun karbe iko da zanga-zanga.

A yau ne 'yan kasar nan su ka shiga rana ta farko daga cikin kwanaki 10 da za a yi ana zanga-zangar adawa da manufofin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Yadda yara su ka rika sata a Kano ya tsorata jama'a

Ezebunwo Nyesom Wike
Zanga-zanga: Yan daban sun fara tare mazauna Abuja Hoto: Ezebunwo Nyesom Wike
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa amma yanzu haka 'yan daba ne su ka yiwa zanga-zangar uwa da makarbiya domin sun fara tare hanyoyi bayan sun kona taya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan daba suna karbar kudi ana zanga-zanga

Mazauna Kubwa da masu bin hanyar wucewa ta yankin sun fada matsala bayan 'yan daba sun fara tare jama'a su na karbar kudi ko su yi masu ta'adi.

'Yan daban da su ka haura 100 sun kona tayoyi a kan titunan, sannan su na fasa motoci da baburan wadanda ba su sanya ganye a jikin ababen hawansu ba.

An gano cewa 'yan daban dauke da makamai na fasa wani bangare na ababen hawan mutanen da su ka ce masu ba su da kudin da za su bayar.

'Yan daba sun hautsina zanga-zanga

A baya mun kawo labarin cewa gwamnatin jihar Kano ta yi zargin cewa wasu marasa kishin jihar sun dauko hayar 'yan daba wadanda su ka hargitsa garin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga a babban birnin tarayya da Legas

Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka ta wani sako da ya tura ga masu zanga-zanga a jihar, inda ya ce 'yan daban da aka shigo da su ne su ka tayar da hankula a Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.