Gwamnatin Kaduna ta Sanya Dokar Hana Fita? Uba Sani ya Magantu Ana Zanga Zanga
- Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya karyata rahoton da ke yawo cewa ya kakaba dokar hana fita ta awanni 24 a jihar saboda zanga zanga
- Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga zanga sun lalata kadarorin gwamnnati da kuma sace dukiyoyin gwamnati da na jama'a
- Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, gwamnan ya ce komai ya dawo dai dai a yanzu, kuma ba a sanya wata doka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Wani rahoto da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana fita ta awanni 24 sakamakon zanga-zanga.
An ce gwamnatin ta sanya dokar ne biyo bayan kona kadarorin gwamnati da satar dukiyar jama'a da 'yan daba suka rika yi ana tsaka da yin gangamin.
An sanya dokar ta-baci a Kaduna?
Sai dai Gwamna Uba Sani ya karyata wannan rahoto, inda ya wallafa a shafin gwamnan jihar a Facebook, ya ce gwamnatin Kaduna ba ta sanya dokar ta baci ba tukunna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Alhamis, Gwamna Uba Sani ya ce tuni gwamnati da jami'an tsaro a jihar suka shawo kan tashin hankalin da ke faruwa a sassan jihar
Jaridar Leadership ta ruwaito gwamnan ya rubuta cewa:
“A yanzu haka da nake magana, ba a sanya dokar hana fita ba a Kaduna. Komai ya dawo dai dai a yanzu."
Kaduna: An kona ofishin KATSLEA
Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu 'yan daba da suka saje da masu zanga-zanga sun kai farmaki ofishin hukumar KASTLEA inda suka cinnawa ginin wuta.
An ce bayan kona wani bangare na ginin, 'yan daban sun kuma wawushe wasu kayayyaki da aka ajiye a ciki, inda daga bisani suka fasa gidaje da shagunan jama'a.
A hannu daya kuma, jami'an 'yan sandan sun fara harbi kan masu zanga-zanga a wasu sassa na jihar Kaduna domin kwantar da tarzoma.
Kalli bidiyon a kasa:
An sanya dokar ta baci a jihohi
A wani labarin, mun ruwaito cewa zuwa yanzu jihohin Arewa uku ne aka sanya dokar hana fita ta awanni 24 bayan fashewar bam da kuma munanar zanga-zanga.
Yayin da Kano da Yobe suka sanya dokar hana fita saboda tashin hankula da aka samu sanadin zanga-zanga, gwamnatin Borno ta sanya dokar ne bayan fashewar bam.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng