Zanga Zanga: Matasa Sun Fandare, Sun Nufi Gidajen Manyan Najeriya a Abuja
- Matasa da ke zanga-zanga a Abuja sun sauya salo inda suka durfafi yankin Asokoro da ke birnin duk da barazanar jami'an tsaro
- Mazu zanga-zangar sun yi yunkurin shiga Asokoro duk da barazana daga jami'an tsaro da kuma harbe-harbe
- Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da gudanar da zanga-zanga a fadin kasar saboda tsadar rayuwa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Masu zanga-zanga a birnin Abuja sun durfafi yankin Asokoro inda ke dauke da manyan kasar Najeriya.
Matasan suna kokarin kutsa kai ne duk da harbe-harben jami'an tsaro yayin da ake cigaba da zanga-zanga.
Zanga-zanga: Matasa sun farmaki Asokoro a Abuja
Daily Trust ta tabbatar da cewa Asokoro ne inda mafi yawan manyan Najeriya da ke mulki ke rayuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan a wurin akwai manyan gine-ginen gwamnati da barikokin sojoji da kuma ofishin DSS.
A cikin wani faifan bidiyon an gano yadda matasan suke cigaba da kutsawa duk da harbin barkwanon tsohuwa domin dakile su.
Zanga-zanga ta rikide a jihohin Arewacin Najeriya
Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da zanga-zanga a fadin kasar da ya rikide ya koma tashin hankali.
A jihohi da dama masu zanga-zangar sun ci karo da matsala yayin da miyagu suka shiga ciki domin biyan bukatar kansu.
Jihohin Kano da Borno da Yobe tuni suka sanya dokar hana fita domin dakile cigaba da barnar da ake yi a zanga-zangar.
'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga
Kun ji cewa jami’an ‘yan sandan kasar nan sun tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga da borkonon tsohuwa a filin Eagle da ke babban birnin tarayya Abuja.
‘Yan sandan sun bayyana cewa sun dauki matakin ne domin tabbatar da umarnin kotu na cewa masu zanga-zanga su tsaya a filin wasa na Moshood Abiola.
Rahotanni sun tabbatar cewa da yawa daga cikin masu zanga-zangar sun nemi mafaka a sassa daban-daban yayain da wasu su ka nuna ko in kula.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng