Kaduna: Masu Zanga Zanga Sun Kona Ofishin KASTLEA, Sun Wawashe Dukiyar Jama’a

Kaduna: Masu Zanga Zanga Sun Kona Ofishin KASTLEA, Sun Wawashe Dukiyar Jama’a

  • Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zanga sun je ofishin hukumar KASTLEA da ke jihar Kaduna inda suka cinna masa wuta
  • An ce masu zanga zangar sun kuma wawushe dukiyar jama'a da ke a cikin ofishin tare da fasa gidaje da ofisoshin makotan hukumar
  • Wannan na zuwa ne yayin da aka fara zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da kuma 'gurbataccen mulki' a fadin kasar nan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Zanga-zangar yunwa ta rikide zuwa tashin hankali a Kaduna yayin da masu zanga-zangar suka kona hedikwatar hukumar KASTLEA tare da wawashe dukiyar jama'a.

Zanga-zangar da aka fara ta da lalama ta rikide ta koma tashin hankali bayan da daruruwan matasa suka mamaye titin Ahmadu Bello daga gidan gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta koma fitina: An kashe mutum 1 yayin da aka babbake gidan mai a Kano

Masu zanga-zanga sun cinnawa ofishin KASTLEA wuta a Kaduna
Kaduna: An kona ofishin KASTLEA tare da wawushe dukiyar jama'a yayin da ake zanga-zanga. Hoto: @Waspapping
Asali: Twitter

An cinnawa ofishin KASTLEA wuta a Kaduna

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa gungun matasan da suka cinnawa ofishin KASTLEA wuta sun kuma wawushe wasu kayan mutane da ke ciki da kuma fasa gidaje da ofisoshin jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan harkokin tsaro da lamuran cikin gida, Mista Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Alhamis.

Wasu hotuna da suka rika yawo a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda aka lallata ofishin KASTLEA yayin da aka kuma kwantar da wani dan sanda har kasa.

Kalli hotunan a kasa:

Zanga-zanga: 'Yan sandan Kaduna sun yi harbi

A hannu daya kuma, jami'an 'yan sandan sun fara harbi kan masu zanga-zanga a wasu sassa na jihar Kaduna domin kwantar da tarzoma.

Wani bidiyo da Channels TV ta wallafa a shafinta na X ya nuna lokacin da masu zanga-zanga ke nunawa 'yan sanda yatsa a kan wani babban titi na jihar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: An yi gumurzu tsakanin yan sanda da matasa a jihar Arewa

A cikin bidiyon, an ga ana sanya wani jami'in dan sanda cikin mota wanda ake zargin masu zanga-zangar ne suka kashe shi (ikirarin da Legit Hausa ba su tabbatar ba.)

Kalli bidiyon a kasa.

An kashe mutum 1 a zanga-zangar Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa an kashe wani matashi mai suna Ismael Ahmad a yankin Hotoro da ke jihar Kano yayin da zanga-zanga ta canja salo a jihar.

An ce akwai wani matashin da shi kuma aka harba amma yana kwance asibitin Aminu Kano ana ceton rayuwarsa yayin da matasa suka kona wani gidan mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.