'Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga Zanga a Babban Birnin Tarayya

'Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga Zanga a Babban Birnin Tarayya

  • Ana tsaka da zzanga-zanga a jihohin Najeriya a birnin Abuja ne aka ji yan sanda sun rika watsawa jama’a borkonon tsohuwa
  • Yan sandan sun tarwatsa masu zanga zangar tare da bukatar su gaggauta komawa wuraren da kotu ta amice su taru
  • Ana zanga-zangar kwanaki 10 da aka fara a yau Alhamis wanda a yanzu haka ya rikide zuwa tashin hankali a wasu wuraen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Jami’an ‘yan sandan kasar nan sun tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga da borkonon tsohuwa a filin Eagle da ke babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan an bindige masu zanga zanga har lahira a ranar farko

‘Yan sandan sun bayyana cewa sun dauki matakin ne domin tabbatar da umarnin kotu na cewa masu zanga-zanga su tsaya a filin wasa na Moshood Abiola.

Nigeria Police Force
An tarwatsa masu zanga-zanga a Abuja Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa da yawa daga cikin masu zanga-zangar sun nemi mafaka a sassa daban-daban yayain da wasu su ka nuna ko in kula da yadda ake watsa masu hayaki masa hawayen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zanga-zanga sun cigaba da sha'aninsu

Rahotanni sun bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, Benneth Igweh ya bayyana cewa an bukaci karin jamai’an tsaro domin tsaurara tsaro.

Wannan ya zo daidai da lamarin da ya afku a yankin Nyanya, yayin da jami’an tsaro a a Mararaba su ka rika jefa hayaki mai sa hawaye tsakanin masu zanga-zangar.

An sake rutsa 'yan zanga-zanga a Legas

Jaridar The Nation ta tattaro cewa an watsawa mutane borkonon tsohuwar a kofar Lekki a Legas.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Tinubu sun yi kishiyar zanga zanga a Kano, su na goyon bayan gwamnati

Rahoton ya bayana cewa amma hakan bai sa masu gudanar da zanga-zangar sun saduda ba, domin sun ci gaba da gudanar da sha’aninsu.

An kashe wasu masu zanga-zanga

A wani rahoton kun ji cewa akalla mutane shida ne ake fargabar an kashe yayin da matasan kasar nan su ka fito tituna domin nuna adawa da manufofin Bola Tinubu.

Wasu mutane sun ji raunuka da dama yayin da ake ganin 'yan kasar nan za su ci gaba da zanga-zanga har ta tsawon kwanaki 10 a fadin Najaeriya, lamarin da ake ganin ya yi kamari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.