Magoya Bayan Tinubu Sun Yi Kishiyar Zanga Zanga a Kano, Suna Goyon Bayan Gwamnati

Magoya Bayan Tinubu Sun Yi Kishiyar Zanga Zanga a Kano, Suna Goyon Bayan Gwamnati

  • Yayin da Najeriya ta rikice da zanga-zanga, wasu masoyan shugaban kasa, Bola Tinubu a Kano sun yi tattakin goyon baya
  • Magoya bayan Tinubu sun bayyana cewa a yi hakuri a ba wa shugaban kasa lokaci wajen tabbatar da gyaran da ya dauko
  • Wadannan mutane sun tabbatar da cewa da gaske akwai tsanani a Najeriya, amma shugaban kasa lokaci ya ke bukata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Magoya bayan Bola Ahmed Tinubu a jihar Kano sun gudanar da zanga-zangar adawa da masu kin manufofin gwamnatin tarayya.

Su na gudanar da zanga-zangar a dai-dai lokacin da 'yan kasar nan ke gudanar da zanga-zangar da ta juye zuwa tashin hankali a kasar nan.

Kara karanta wannan

Sufetan 'yan sanda ya fadi shirin da miyagu su ka yi yayin zanga zangar lumana

Bola Ahmed
Magoya bayan Tinubu sun yi tattakin adawa da zanga zanga a Kano Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa magoya bayan sun bayyana cewa shugaban kasa ya na da manufofin ingata ci gaban 'yan Najeriya matukar za a ba su lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tinubu ya na kokari," Magoyan bayan Tinubu

Daya daga cikin magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu sun bayyana cewa an dauko hanyar gyara kuma al'amura za su gyaru.

Abdullahi Muhammad Saleh, daga cikin masu goyon bayan zanga-zangar marawa Tinubu baya ya ce sun fito ne domin shaidawa shugaban kasar cewa su na sane da ayyukansa.

Daily Post ta wallafa cewa duk da magoya bayan sun aminta da cewa akwai matsala a kasar nan, amma ana kokarin ganin shawo kan matsalar.

"Ba mu son masu muguwar aniya su shiga cikin zanga-zanga domin jawo hargitsi. Ba mu goyon bayan zanga-zangar tashin hankali."

An tarwatsa masu zanga-zanga a Bauchi

Kara karanta wannan

Ana fargabar miyagu za su shiga zanga zanga, an samu hanyoyi 5 domin kare kai

A baya mun ruwaito cewa jami'an 'yan sanda sun yi nasarar tarwatsa dandazon matasa masu zanga-zanga kofar gidan Sarkin Bauchi ta hanyar amfani da borkonon tsohuwa.

Masu zanga-zangar sun kutsa fadar sarkin Bauchin domin neman ganawa da shi, amma jami'an tsaro sun hana su karasawa cikin gidan sarkin ganin yadda lamari ke daukar dumi a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.