Kano: ’Yan Sanda Sun Tashi Tsaye, Matasa Sun Farmaki Shaguna Daga Fara Zanga Zanga
- An fara samun matsala a Kano yayin zanga-zanga bayan wasu matasa sun yi yunkurin fasa shaguna a birnin
- An tabbatar da cewa matasan sun kai farmakin ne a 'Zoo Road' da ke birnin Kano inda suka fasa wasu tagogi
- Sai dai rundunar 'yan sanda ta yi nasarar dakile barnan inda ta kora matasan da suka yi kokarin jawo matsala a wurin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta tarwatsa wasu matasa da suka yi kokarin fasa wuraren adana kaya.
'Yan sanda sun dauki matakin ne a 'Zoo Road' da ke birnin Kano da safiyar yau Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.
'Yan sandan Kano sun tarwatsa masu 'zanga-zanga'
Wadanda ake zargin sun yi kokarin kutsawa cikin babban kantin Sadaraki da ke gidan sama kafin 'yan sanda su ankara, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai an tabbatar da cewa kafin zuwan jami'an tsaro matasan har sun farfasa tagogin gine-ginen da ke wurin.
A halin da ake ciki yanzu, mutane da dama sun kasance a gidajensu yayin zanga-zangar da ake a fadin kasar.
Matasa sun fito zanga-zanga a jihar Kano
Wannan na zuwa ne yayin da wasu matasa suka fito zanga-zanga a jiya Laraba 31 ga watan Agustan 2024 a Kano.
Matasan suna nuna kin jinin zanga-zangar da za a fita a yau Alhamis 1 ga watan Agustan 2024 a fadin kasar.
Wadanda suka fito zanga-kan titunan sun nuna damuwa kan yadda ake samun matsala duk lokacin da aka gudanar da zanga-zangar.
Sanusi II ya gargadi masu zanga-zanga
A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana mai kama hankali kan shirin gudanar da zanga-zanga a Najeriya.
Mai martaba Sanusi II ya shawarci matasa da su guji shiga lamarin zanga-zangar da aka shirya fita gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.
Wannan na zuwa ne yayin da aka fita zanga-zanga da safiyar yau Alhamis 1 ga watan Agustan 2024 a fadin kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng