Yadda Hukumar EFCC Ta Kwato N232bn, $70m Cikin Shekara 1 Kacal

Yadda Hukumar EFCC Ta Kwato N232bn, $70m Cikin Shekara 1 Kacal

  • Hukumar EFCC ta samu nasara mai girma a yaƙin da take yi da masu karɓar cin hanci da sauran laifukan rashawa a ƙasar nan
  • EFCC ta samu nasarar ƙwato N232bn da $70m a tsakanin watan Mayun 2023 zuwa watan shekarar 2024 kamar yadda aka sanar
  • Bayan waɗannan kuɗaɗen hukumar ta kuma yi nasarar ƙwato wasu kuɗi masu yawa na ƙasashen waje duk a cikin shekara ɗaya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar EFCC, ta samu nasarar ƙwato kusan N232bn da wasu kuɗaɗen masu yawa a cikin shekara ɗaya.

Hukumar mai yaƙi da cin yanci da rashawar ta ƙwato kuɗaɗen ne a tsakanin watan Mayun 2023 zuwa watan Mayun 2024.

Kara karanta wannan

Hukumar zabe ta sa lokacin zaben ciyamomi a Kano, ta kafa sharudda ga 'yan takara

EFCC ta kwato N232bn
Hukumar EFCC ta kwato N232bn cikin shekara daya Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

EFCC ta samu nasara cikin shekara 1

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa wata takarda da ta gani daga hukumar ce ta tabbatar da hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takardar ta yi bayani a taƙaice kan laifukan da hukumar ta bincika da kuɗaɗen da aka ƙwato cikin shekara ɗaya, amma ba ta bayar da cikakken bayani ba.

Wani babban jami’in hukumar ya tabbatar da sahihancin takardar a wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Leadership.

A cewar takardar, EFCC ta samu ƙorafe-ƙorafe guda 15,753 a cikin shekara ɗaya.

Sai dai bayan binciken laifuffuka 23,287, hukumar ta shigar da kararraki 5,376 a gaban kotu da suka shafi mutane da kamfanonin da ake zargi.

Shari'ar da aka yi a EFCC a kotu

A cikin wannan wa'adin, lauyoyin da ke kare hukumar sun yi nasara kan ƙararraki 3,376.

Kara karanta wannan

Mutanen Kano sun shiga sabuwar matsala kwana 1 gabanin fara zanga zanga

Sai dai ba a bayyana cewa ko dukkanin ƙararrakin an shigar da su a tsakanin watan Mayun 2023 zuwa watan Mayun 2024 ba ne.

Menene adadin kuɗin da EFCC ta ƙwato?

Kuɗin da hukumar ta samu nasarar ƙwatowa a cikin shekara ɗaya sun haɗa da N231,623,186,004.74, $70,260,544.18, da £29,264.50.

Sauran su ne €208,297.10 (Yuro), ₹ 51,360 (Rufin Indiya), $3,950 (Dalar Canada) $740 (Dalar Australia), Rand 35,000 na Afirika ta Kudu, 42,390 UAE Dirham, Riyal 247 (Saudiyya) da ¥74,754 (Yun na China).

Karanta wasu labaran game da EFCC

EFCC ta fallasa masu yi mata maƙarƙashiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta bayyana masu hannu a zanga-zangar da ake shirin yi domin nuna adawa da ayyukanta.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun sake dasa bam, ya hallaka babban jami'in gwammnati a Borno

Hukumar EFCC ta ce wani tsohon gwamna da wasu tsofaffin ministoci biyu ne ke da hannu a zanga-zangar da ake shirin shiryawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng