'Yan Sanda Sun Sha Sabon Alwashi Kan Zanga Zanga Bayan Nasarar Gwamnati a Kotu

'Yan Sanda Sun Sha Sabon Alwashi Kan Zanga Zanga Bayan Nasarar Gwamnati a Kotu

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya za ta tabbatar da bin umarnin kotu na taƙaita zanga-zanga a wasu tsirarun wurare kadai
  • Jihohi da dama sun samu umarnin kotu wanda ya umarci masu zanga-zanga da su gudanar da ita a wasu keɓaɓɓun wurare
  • A ranar Alhamis, 1 ga watan Agustan 2024 ne za a fara gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Rundunar ƴan sanda ta sha alwashin aiwatar da umarnin kotu na takaita zanga-zanga zuwa keɓaɓɓun wurare.

Hakan na zuwa ne dai yayin da matasa suka yi niyyar fara zanga-zanga a faɗin ƙasar nan kan halin ƙunci da tsadar rayuwar da ake fama da su a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

IGP ya umarci ƴan sanda su ɗauki mataki mai tsauri kan abubuwa 2 a lokacin zanga zanga

'Yan sanda za su takaita zanga-zanga
'Yan za su ba masu zanga-zanga kariya Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Shugaban 'yan sanda ya gana da masu zanga-zanga

Babban Sufetan ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya yi taro da masu shirya zanga-zangar inda ya buƙaci ka da su hau tituna, amma sun yi fatali da wannan buƙatar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, awanni kafin fara zanga-zangar, jihohi daban-daban sun samu umarnin kotu wanda ya taƙaita gudanar da zanga-zangar a wasu wurare.

Jihohin Kwara, Ogun, Legas da birnin tarayya Abuja sun samu umarnin kotu wanda ya umarci masu zanga-zangar su yi ta a wasu wurare.

Ƴan sandan Legas za su bi umarnin kotu

Da yake martani kan hakan, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa za a aiwatar da umarnin na kotu a jihar, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

"Mun samu umarni daga kotu wanda ya taƙaita zanga-zanga a Gani Fawehinmi Freedom Park, hanyar Ikorodu, Ojota da Peace Park, Ketu, daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa ƙarfe 6:00 na yamma a ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agusta, 2024.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bayyana tagomashin da masu zanga zanga za su samu, sun kafa sharadi

"Rundunar ƴan sandan Najeriya a matsayinta na hukumar tabbatar da doka da oda, za ta aiwatar da wannan umarnin yadda ya kamata."
"A bisa hakan, rundunar na ba da tabbaci ga duk mai son shiga zanga-zangar cewa za a samar da cikakken tsaro a wuraren da aka bayyana."

- SP Benjamin Hundeyin

Umarnin shugaban ƴan sanda kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban sufetan ƴan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, ya umarci jami'ai su ɗauki tsattsauran mataki kan masu ƙone-ƙone da tada zaune tsaye a lokacin zanga-zanga.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da IGP Kayode ya sa wa hannu da kansa gabanin fara zanga-zangar gama gari kan tsadar rayuwa a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng