Kano: Abba Kabir Ya Gwangwaje Buba Galadima da Mukami, Ya Yi Wasu Nade Nade

Kano: Abba Kabir Ya Gwangwaje Buba Galadima da Mukami, Ya Yi Wasu Nade Nade

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi sababbin nade-nade da suka shafi bangaren ilimi a kokarinsa na inganta harkokin ilimi jihar
  • Gwamna Abba Kabir ya amince da nadin jigon jamiyyar NNPP, Buba Galadima a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na Kwalejin Fasaha
  • Abba ya kuma amince da nadin tsohon mataimakin gwamnan Kano, Farfesa Hafiz Abubakar shugaban kwamitin gudanarwa na Jmai'ar Bayero

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya yi sabbin nade-nade a jihar domin inganta harkokin ilimi da shugabanci.

Gwamna Abba ya amince da nadin jigon jam'iyyar NNPP, Buba Galadima a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na Kwalejin Fasaha da ke Kano.

Kara karanta wannan

Tsaftar muhalli: Abba Kabir ya dauki hanyar gyara bayan maganar hadimin Buhari

Abba Kabir ya nada Buba Galadima mukami a jihar Kano
Gwamna Abba Kabir ya ba Buba Galadima mukami a Kwalejin Fasaha da ke Kano. Hoto: @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Abba Kabir ya ba Buba Galadima mukami

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Baba Halilu Dantiye ya fitar da @babarh ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran mamboibn kwamitin sun hada da Injiniya Rashida Musa da Dakta Usman Abbas da Farfesa Dahiru Sani Shu'aibu wanda zai wakilci Jami'ar Bayero.

Sai kuma wakilai biyu daga hukumar makaranta da kuma wakili daya daga kowace makaranta da ke karkashin Kwalejin Fasaha.

Kano: Abba ya nada Farfesa Hafiz mukami

Gwamna Abba ya kuma nada tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Hafiz Abubakar shugaban kwamitin gudanarwa na Jami'ar Bayero.

Sai Hon. Nura Dankadai da Hajiya Mariya Ali Kote da Dakta Kabir Kofa da Farfesa Mustapha Hussain za su kasance mambobi.

Kwamishinan yada labarai, Halilu Dantiye ya ce duka nadin mukaman za su fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

Ana cikin tsadar rayuwa, gwamma zai rushe sabon gidan gwamnatin biiliyoyin Naira

Kano: Sanusi II ya magantu kan zanga-zanga

Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana mai kama hankali kan shirin gudanar da zanga-zanga a Najeriya.

Sanusi II ya shawarci matasa da su guji shiga lamarin zanga-zangar da aka shirya fita gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.

Basaraken ya ce ya ji zancen fara shirin zanga-zangar a kafofin sadarwa cewa za a fara ta ne kusa da fadarsa da ke jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.