Sanusi II Ya Yi Magana Kan Zanga Zanga, Ya Fallasa Hassadar da Ake Yi Wa Jihar Kano

Sanusi II Ya Yi Magana Kan Zanga Zanga, Ya Fallasa Hassadar da Ake Yi Wa Jihar Kano

  • Yayin da ake shirin fita zanga-zanga, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gargadi matasa kan shiga harkar da ba ta da tsari
  • Sanusi II ya yi gargadi inda ya ce kwata-kwata babu tsari a zanga-zangar tun da ba a san wadanda suka shirya ta ko daukar nauyinta ba
  • Sarkin ya kuma bayyana damuwa kan yadda jihar Kano ke fama da mahassada ta kowane bangare ganin irin cigaban da suke da shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magan mai kama hankali kan shirin gudanar da zanga-zanga a Najeriya.

Sanusi II ya shawarci matasa da su guji shiga lamarin zanga-zangar da aka shirya fita gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta barke a Kano ana daf da fita ta gama gari, bayanai sun fito

Sarkin Kano, Sanusi II ya gargadi masu zanga-zanga a Najeriya
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi martani kan shirin zanga-zanga. Hoto: @masarautarkano.
Asali: Twitter

Zanga-zanga: Muhammadu Sanusi II ya shawarci matasa

Basaraken ya ce ya ji zancen fara zanga-zangar a kafofin sadarwa cewa za a fara ta ne kusa da fadarsa da ke Kano, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sai dai bai san su waye ne ke shirya zanga-zangar ba ko masu daukar nauyinta inda ya ce shiga cikinsu hatsari ne.

Har ila yau, Sarki Sanusi II ya bayyana yadda 'yan Kano suke fuskantar hassada daga bangarori daban-daban inda ya ce suna da makiya sosai.

Sarkin ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim ya wallafa a shafin X.

Sarki Sanusi II ya fadi burinsa ga 'yan Kano

A cikin faifan bidiyon, Sarkin ya ce yana son ya zama malamin Kano ya fi na kowa, haka gwamnan Kano da 'yan kasuwa da sarakunan Kano su fi na kowa.

Kara karanta wannan

"Ka samar mana da motoci": Masu zanga zanga sun tura bukatunsu ga gwamna

"Duk wanda Allah ya yi wa ni'ima dole ya yi hakuri da hassada, muna da makiya idan dan kasuwanmu ya yi suna za a nemi karya shi, haka idan malaminmu ne ya yi suna."
"Idan mai sarauta ya kasaita za a yi kokarin karya shi, amma wannan albarka idan dai ta zauna, albishir na farko shi ne wallahi Kano babu yadda za a yi da mu."

- Muhammadu Sanusi II

Zanga-zanga: APC ta yi kira ga 'yan Kano

Kun ji cewa jigon jam'iyyar APC a jihar Kano ya roki 'yan jihar da su guji fitowa zanga-zanga da ake shirin yi a fadin kasar.

Nasiru Bala Ja'oji ya ce nuna damuwa kan tsare-tsaren gwamnati ba matsala ba ne amma ta hanyar rigima bai kamata ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.