Kotu Ta Yi Hukunci Kan Masu Shirin Zanga Zanga, Ta Gindaya Sharuda Masu Tsauri
- Ana shirin fita zanga-zanga a jihar Ogun, Babbar Kotun jihar ta yi hukunci, inda ta ba matasa umarni kan lamarin
- Kotun ta umarci masu gudanar da zanga-zangar da su yi a wurare guda hudu kacal a jihar bayan shigar da korafi gabanta
- Legit Hausa ta ji ta bakin wani shugaban kungiyar matasa kan wannan hukunci na kotu a jihar Ogun kan zanga-zangar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun - Babbar Kotun jihar Ogun ta yi zama kan masu zanga-zanga a jihar inda ta ba su umarni yadda za su gudanar da ita.
Kotun ta umarce su da su gudanar da zanga-zangar a wurare hudu kacal a fadin jihar sabanin yadda suka shirya.
Zanga-zanga: Kotu ta gidanya sharuda ga matasa
Punch ta tabbatar da cewa kotun ta rage lokacin gudanar da zanga-zangar daga 8.00 na safe zuwa karfe 5.0O na yamma a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkalin kotun. Mai Shari'a, O. Ogunfowora shi ya dauki wannan mataki a yau Laraba 31 ga watan Yulin 2024, cewar TheNigeriaLawyer.
Ogunfowora ya umarce su da yin zanga-zangar a filin wasa na MKO Abiola da makarantar Ansar-ud-Deen da ke Ota.
Sauran wuraren sun hada da babbar makarantar Remo da ke Sagamu da kuma filin wasa na Dipo Dina da ke Ijebu-Ode.
Wannan na zuwa ne bayan korafin da kwamishinan shari'a a jihar, Oluwasina Ogungbade ya shigar a gaban kotun.
Tattaunawar Legit Hausa da wani matashi
Legit Hausa ta ji ta bakin wani shugaban kungiyar matasa kan wannan hukunci na kotu a Ogun.
Kwamred Kabir Haruna ya ce kwata-kwata hakan bai dace ba saboda dakile shirin kwatar ƴanci ne.
"Wannan wata hanya ce ta kashe karfin guiwar matasa idan aka ce sai wasu zababbun wurare za a yi zanga-zanga."
"Musabbabin gudanar da zanga-zangr shi ne gwamnatin ta san da halin da jama'a ke ciki."
- Kabir Haruna
Matasa sun fito zanga-zanga a Kano
Kun ji cewa daruruwan mutane a jihar Kano sun fito kan tituna inda suke adawa da zanga-zangar da za a yi a gobe.
Mutanen sun cika titunan birnin ne a yau Laraba 31 ga watan Agustan 2024 domin nuna rashin goyon baya ga zanga-zanga.
Kungiyar da ke goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ta tabbatar da cewa shugaban yana kokarin kawo sauki a kasar baki daya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng