Gwamnatin Tinubu ta Fadi Abin da ke Firgita ta Game da Zanga Zanga

Gwamnatin Tinubu ta Fadi Abin da ke Firgita ta Game da Zanga Zanga

  • Da alama kokarin gwamnatin tarayya na hana zanga-zanga a gobe Alhamis bai samu nasarar da aka buƙata ba
  • Gwamnatin ta ce dama ba wai ta na son tauye 'yancin 'yan Najeriya na gudanar da zanga-zanga ba ne
  • A cewar sakataren gwamnati, George Akume, sun gano 'yan kungiyar ta'adda za su iya shiga cikin masu zanga-zanga a tayar da yamutsi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana fargabarta game da zanga-zangar gama gari da za a fara a ranar Alhamis, 1 Agusta, 2024.

Daga 1-10 Agusta, 2024 ne wasu 'yan kasar nan su ka ce za su gudanar da zanga-zanga saboda halin yunwa da tsadar farashin abinci.

Kara karanta wannan

Saura kiris a fara zanga zanga, gwamnan Yobe ya sa labule da shugabannin hukumomin tsaro

Senator Dr. George Akume
Gwamnatin tarayya ta ce matsalar tsaro ce ta sa ta nemi a hakura da zanga-zanga Hoto: Senator Dr. George Akume
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sakataren gwamnati, George Akume ya ce duk da gudanar da zanga-zanga 'yancin 'yan kasa ne, amma sun hango matsala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'"Yan bindiga za su shiga zanga-zangar," Gwamnati

Gwamnatin tarayya ta ce ta hango barazanar tsaro tattare da zanga-zangar gama gari da wasu 'yan kasar nan za su tsunduma.

Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya ce akwai babbar barazanar 'yan bindiga da 'yan boko haram za su shiga rigar masu zanga-zanga a tafka barna.

Ya ce wannan damuwar ce ta sa gwamantin tarayya ke rokon matasa su yi watsi da aniyarsu ta shiga zanga-zanga, The Cable ta wallafa.

Menene zai fi zanga-zanga alheri?

Gwamnatin tarayya ta bukaci matasan kasar nan su rungumi tsarin tattaunawa da gwamnati a madadin zanga-zanga. Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ne ya ce hakan zai fi zanga-zanga alheri ganin barazanar tsaro da ke tattare da fita tituna a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta shata layi, ta hana masu zanga zanga zuwa wasu wurare idan an fito titi

Gwamnati ta shirya tunkarar zanga-zanga

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Yobe ya yi shirin wanzar da zaman lafiya yayin gudanar da zanga-zangar kwanaki 10 da za a fara daga gobe.

Gwamnan jihar, Mai Mala Buni ya zauna da shugabannin hukumomin tsaro domin bullowa lamarin tsaro a sassan jihar idan an fara zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.