Hukumar Zabe Ta Sa Lokacin Zaben Ciyamomi a Kano, Ta Kafa Sharudda Ga 'Yan Takara

Hukumar Zabe Ta Sa Lokacin Zaben Ciyamomi a Kano, Ta Kafa Sharudda Ga 'Yan Takara

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Kano ta shirya gudanar da zaɓen ƙananann hukumomi a jihar kamar yadda ake sa rai
  • Hukumar zaɓen ta sanya ranar 30 ga watan Nuwamban 2024 domin gudanar da zaɓen a ƙananan hukumomi 44 na jihar
  • A wannan karon hukumar za ta yi wa ƴan takarar gwajin miyagun ƙwayoyi kafin ba su damar tsayawa takara a zaɓen

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano ta tsayar da ranar 30 ga watan Nuwamba, 2024, a matsayin ranar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.

Hakan na zuwa ne biyo bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke, inda ta ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu tare da umartar jihohi su samar shugabannin ƙananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Mutanen Kano sun shiga sabuwar matsala kwana 1 gabanin fara zanga zanga

Za a yi zaben kananan hukumomi a Kano
Za a yi zaben kananan hukumomi a Kano a watan Nuwamba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A kwanakin baya ne gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na gudanar da zaɓen nan ba da daɗewa ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Kano, shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ya bayyana shirin hukumar na gudanar da zaɓen, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Za a yi wa ƴan takara gwajin kwayoyi

Sai dai shugaban ya yi nuni da cewa, za a yiwa duk wani ɗan takarar da zai tsaya takara a zaɓen gwajin miyagun ƙwayoyi kafin a ba shi damar yin takara.

A cewar shugaban hukumar zaɓen, za a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu daga ranar 6 ga watan Satumba zuwa 18 ga watan Oktoba.

Hukumar za ta fitar da sunayen ƴan takara da suka cancanta a ranar 25 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Dubun dan majalisa, hakimai masu hada baki da 'yan bindiga ta cika a jihar Arewa

Jam'iyyun siyasa za su samu har zuwa ranar 1 ga Nuwamba domin cirewa ko sauya ƴan takara.

Yaushe aka yi zaɓen ciyamomi na ƙarshe?

An dai gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na ƙarshe ne a jihar a ranar 16 ga watan Janairun 2021 a ƙananan hukumomi 44 da gundumomi 484.

A halin yanzu, ƙananan hukumomi 44 na jihar suna ƙarƙashin jagorancin shugabannin riƙon kwarya da ke kula da ayyukansu.

Gwamna Abba ya ƙaddamar da kwamiti

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da kwamiti kan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata na ƙasa.

Ƙaddamar da kwamitin na zuwa ne sa’o’i 48 kacal bayan da Shugaba Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng