Zanga Zangar Adawa da Tinubu Ta Samu Gagarumar Matsala Awanni Kafin a Fara

Zanga Zangar Adawa da Tinubu Ta Samu Gagarumar Matsala Awanni Kafin a Fara

  • Zanga-zangar da ake shirin yi domin nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan ta gamu da cikas a jihar Kwara
  • Wasu ƙungiyoyin ɗalibai, matasa da naƙasassu sun janye daga shiga zanga-zangar wacce aka shirya gudanarwa a Agusta
  • Ƙungiyoyin sun yi nuni da cewa kamata ya yi a bi hanyar tattaunawa domin samar da mafita kan halin da ake ciki a yau

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Ɗalibai, 'yan ƙungiyoyin KPMO, masu nakasa da sauran ƙungiyoyin matasa a jihar Kwara sun janye daga zanga-zangar da za a yi a faɗin ƙasar nan.

Sun bayyana cewa zanga-zangar ba ita ce mafita ba, inda suka buƙaci a tattuna domin samar da mafita kan halin ƙuncin da ake ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jerin jihohin da za a gudanar da zanga zanga a ranar 1 ga watan Agusta

Matasan Kwara sun fice daga zanga-zanga
Kungiyoyin matasa da dalibai sun fice daga zanga-zanga a Kwara Hoto: Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Ƙungiyoyin sun bayyana matsayarsu ne a yayin wani taron manema labarai a birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyoyi sun fice daga zanga-zanga

Shugaban ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) reshen jihar Kwara, Issa Abdulgafar Arikewuyo, shugaban ƙungiyar KPMO, Beki Mashood, sun buƙaci ɗaliban jihar da matasa ka da su shiga zanga-zangar da za a yi rikici.

Issa Abdulgafar Arikewuyo ya bayyana cewa sun yanke shawarar tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samun zaman lafiya.

"Abin da muka yi amanna da shi, shi ne jihar Kwara an santa da zaman lafiya kuma a shirye muke domin ganin hakan ya ci gaba da tabbata."
"A lokacin zanga-zangar baya, da yawa daga cikin iyayenmu sun sha wahala saboda an yi musu sata a wuraren kasuwancinsu, kuma da yawansu har yanzu ba su fargaɗo ba. Ba mu son tarihi ya sake maimaita kansa."

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta kara alawus din 'yan NYSC zuwa N77,000? An gano gaskiya

"Haka kuma zanga-zangar ta shafi matasa da ɗalibai saboda an lalata ɗan kasuwancin da suke yi domin tsira da rayukansu sakamakon rikicin da ya ɓarke."
"Hakan ya sanya da yawansu suka haƙura da karatu saboda ba za su iya biyan kuɗaɗen makaranta ba."

- Issa Abdulgafar Arikewuyo

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

Akpabio ya tayar da ƙura kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya tsokani masu goyon bayan zanga-zangar da ake shirin yi kan tsadar rayuwa.

Sanata Godswill Akpabio ya ce duk wanda ke marawa shirin zanga-zangar yunwa baya zai iya tafiya a yi da shi amma, "mu kam mu na nan mu na cin abinci."

Kara karanta wannan

Ana harin zanga zanga, gwamnatin tarayya ta dauki muhimmin mataki

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng