Bayan Hango Kwantacciyar Barazana, Jagoran Zanga Zanga Ya Ajiye Jagoranci
- An fara rage karfin gwiwar matasa yayin da wasu kungiyoyin ke juya baya ga shirin fita zanga zangar adawa da tsadar rayuwa
- Rahotanni na nuni da cewa jagoran zanga zangar a Sokoto ya ce ba zai cigaba da jagorantar matasa a jihar ba a halin yanzu
- Jagoran, Bashir Binji ya bayyana dalilan da suka sa ya ajiye fita zanga zangar da kuma barazanar da za a iya fuskanta a jihar Sokoto
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - An samu koma baya yayin da jagoran zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ya juya baya a Sokoto.
Bashir Binji ya bayyana cewa ya ajiye zanga zangar ne domin ganin bai jawo tashin hankali a jihar Sokoto ba.
Jaridar the Cable ta wallafa cewa Bahsir Binji ya yi jawabi ne a jiya Talata ga manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin barin zanga zanga a Sokoto
Shugaban masu zanga zanga a jihar Sokoto, Bashir Binji ya bayyana cewa sun samu rahoto daga jami'an tsaro kan za a kai hari a lokacin zanga zangar.
Saboda haka Bashir Binji ya ce sun dakatar da fita zanga zangar domin kaucewa kawo tashin hankali a Sokoto.
Wuraren da za a kai hari a Sokoto
Jaridar PM News ta wallafa cewa Bahsir Binji ya ce jami'an tsaro sun tabbatar da cewa za a kai hari kasuwanni a lokacin zanga zangar.
Bayan haka, an ruwaito cewa bayanan jami'an tsaro sun nuna cewa akwai niyyar kai hari a bankuna da wasu wuraren gwamnati.
Yadda aka gano shirin kai hari a Sokoto
Shugaban yan kasuwa a jihar Sokoto, Abubakar Sarkin Gishiri ne ya samu labarin cewa za a kai hari a wasu wurare a jihar.
Biyo bayan haka, Abubakar Sarkin Gishiri ya tuntubi jami'an tsaron farin kaya kuma suka tabbatar masa da lamarin.
Zanga zanga: Matasa sun gana da yan sanda
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun bukaci masu shirya zanga zangar adawa da tsadar rayuwa su bayyana sunayensu kafin samun izinin hukuma.
Wasu daga cikin jagororin zanga zanga a Najeriya sun ba rundunar yan sanda bayanansu kuma sun tattauna da rundunar a ranar Talata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng