"Muna Can Muna Cin Abinci," Shugaban Majalisa Ya Ta da Ƙura Kan Zanga Zangar Ake Shirin Yi
- Shugaban majalisar dattawa ya tada ƙura, ya tsokani masu shirin fita zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya
- Sanata Godswill Akpabio ya ce duk wanda ya ga zai fita zanga-zanga ga hanya nan amma su suna can suna cin abinci, ba abin da ya dame su
- Akpabio ya bayyana cewa ba ya goyon bayan sauya gwamnati, inda ya ja hankalin ƴan Najeriya su marawa gwamnati mai ci baya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya tsokani masu goyon bayan zanga-zangar da ake shirin yi kan tsadar rayuwa.
Sanata Akpabio ya ce duk wanda ke marawa shirin zanga-zangar yunwa baya zai iya tafiya a yi da shi amma, "mu kam muna nan muna cin abinci."
The Cable ta ce Godswill Akpabio ya yi wannan furuci ne a wurin wani taro da Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ta shirya ranar Talata a jihar Ribas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman nasa na zuwa ne a lokacin da matasa ke shirye-shiryen fara zanga-zanga kan yunwa da tsadar rayuwa a rana 1 kuma su ƙarƙare a ranar 10 ga watan Agusta.
IGP ya gana da jagororin zanga-zanga
Babban Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya gana da wasu daga cikin masu shirya zanga-zangar jiya Talata a Abuja, Daily Truat ta rahoto.
Shugaban ƴan sandan ya roke su da su yi zanga-zangar a wuri ɗaya domin kaucewa tada zaune tsaye, amma jagororin masu zanga-zangar sun ce ba za ta saɓu ba.
Akpabio ya tsokani masu zanga-zanga
Da yake jawabi a wurin taron a Ribas, shugaban majalisar dattawa ya ce:
"Dukan mu muna shan wahala a halin da ake ciki a yanzu, amma mun san cewa ba za a dawwama a haka ba, wahala ce ta ɗan looaci."
"MD ina ƙara gode maka bisa kalaman da ka faɗa, ka faɗa mana babu bukatar sauya gwamnati, kamata ya yi mu rungumi wannan gwamnati mai ci."
"Masu son yin zanga-zanga za su iya fita amma mu muna can muna cin abinci. Dole ne na kara gode wa yankin Neja Delta."
Wani sarki ya magantu kan zanga-zanga
A wani rahoton kuma wani Sarkin yarbawa ya yi kira ga masu shirin yin zanga-zanga kan tsaɗar rayuwa su yi haƙuri su karawa gwamnatin Bola Tinubu lokaci.
Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya ce wahalhalu da tsadar rayuwar da mutane ke kuka a kai, al'amari ne da ya shafi duk duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng