Hankalin Majalisa Ya Kai Kan N4.2bn da Aka Ware Domin Biyan Albashi a Kamfanin da Bai Aiki

Hankalin Majalisa Ya Kai Kan N4.2bn da Aka Ware Domin Biyan Albashi a Kamfanin da Bai Aiki

  • Kwamitin majalisar dattawa da ke bincike kan zargin almundahana a kamfanin ƙarafa na Ajaokuta ya yi zama a ranar Talata
  • A yayin zaman kwamitin, Sanata Natasha Akpoto Uduaghan ta nemi jin ba'asi kan N4.2bn da aka ware a kasafin kuɗin shekarar 2024
  • An ware makudan kudin domin biyan ma'aikata albashi duk da kamfanin bai aiki na tsawin shekara da shekaru a Najeriya
  • Sanatar ta ce a matsayin na ƴar yankin a ziyarce-ziyarcen da ta kai kamfanin da wuya take iyan ganin mutane 10

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta nemi jin ba'asi kan N4.2bn da aka ware a cikin kasafin kuɗin 2024 a matsayin kuɗin albashin ma’aikata na kamfanin ƙarafa na Ajaokuta.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya ce ba zai iya biyan sabon mafi karancin albashi ba, ya fadi dalili

Kamfanin ya ci gaba da kasancewa wanda ba ya aiki duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na farfaɗo da shi.

Majalisar dattawa na bincike kan kamfanin Ajaokuta
Majalisar dattawa na bincike kan zargin almundahana a kamfanin Ajaokuta Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Neman jin ba'asin adadin ma'aikatan da za su samu albashi daga cikin N4.2bn ya faru ne a lokacin wani zaman kwamitin bincike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta na zargin an yi a almundahana a kamfanin karafunan daga shekarar 2002.

Sanata ta titsiye shugaban kamfanin Ajaokuta

Mataimakiyar shugaban kwamitin kuma sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta titsiye shugaban kamfanin Summaila Abdul Akaba.

An tattauna kan ma’aikatan da ke karɓar albashi da za a biya N4.2bn, cewar rahoton The Guardian.

Ta ce, kasancewarta ƴar yankin ce, ta yi burin ganin an farfaɗo da kamfanin, inda ta ƙara da cewa a ziyarar da ta kai kamfanin, da ƙyar ta samu mutane 10, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Ana harin zanga zanga gwamnati ta amince da ba da aikin da zai lakume N81bn

"Shugaban kamfanin ƙarafa na Ajaokuta, ina da tambaya mai kyau a gare ka a matsayina na ƴar asalin yankin, na damu matuƙa da halin da kamfanin yake ciki kuma ina da burin ganin kamfanin ya farfaɗo."

"An ware N4.2bn na albashin ma’aikata a shekarar 2024, amma daga ziyarce-ziyarcen da na kai kamfanin, da kyar za a ga mutum 10."
"Saboda haka su waye ma’aikatan da suke karɓar albashi duk wata daga N4.2bn ɗin da aka ware?"
"A ƙididdiga, idan ana biyan N300,000 a kowane wata ga mutane 14,000 na shekara guda, za a samu N4.2bn ko N500,000 ga mutane 8,400 a kowane wata a shekara."
"Ina ma'aikata 14,000 ko 8,400 a Ajaokuta da ake kashewa N4.2bn da aka ware?"

- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Akwai lauje cikin naɗi a Ajaokuta

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa kuma Sanata mai wakiltar Enugu ta Yamma, Osita Ngwu, ya hana shugaban kamfanin amsa tambayar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rattaɓa hannu a dokar sabon mafi ƙarancin albashi, bayanai sun fito

"Don Allah, kar mu sanya kanmu cikin matsala, domin wannan kasafin kuɗin majalisa ce ta amince da shi."

- Sanata Osita Ngwu

Majalisar dattawa ta kira zaman gaggawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya kira taron gaggawa na majalisar kan muhimmin batu da ya shafi ƙasa.

Magatakardan majalisar dattawan, Chinedu Akubueze ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 29 ga watan Yuli, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng