Jagororin Zanga Zanga Sun Cire Tsoro Sun Bayyana Kansu ga Shugaban Yan Sanda

Jagororin Zanga Zanga Sun Cire Tsoro Sun Bayyana Kansu ga Shugaban Yan Sanda

  • Yan sanda sun bukaci masu shirya zanga zangar adawa da tsadar rayuwa su bayyana sunayensu kafin samun izinin hukuma
  • Wasu daga cikin jagororin a Najeriya sun ba rundunar yan sanda bayanansu kuma sun tattauna da rundunar a ranar Talata
  • Sufeton 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya bayyana abubuwan da suka tattauna da jagororin zanga zanga a zaman da suka yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wasu daga cikin jagororin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa sun bayyana a gaban yan sandan Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan buƙata da rundunar yan sanda ta yi na samun bayanan jagororin zanga zangar lumanar da za ayi.

Kara karanta wannan

'Yan daban Legas sun marawa gwamnati baya, sun yi barazana ga masu shirin zanga zanga

Yan sanda
Jagororin zanga zanga sun bayyana kansu ga yan sanda. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Legit ta gano cewa an tattauna tsakanin yan sanda da jagororin zanga zangar ta yanar gizo a cikin sakon da rundunar yan sanda ta wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagororin zanga-zanga sun hadu da 'yan sanda

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa lauya Femi Falana da Ebun-Olu Adegboruwa su ne suka tattauna da ita a matsayin jagororin zanga zangar

Lauya Inibehe Effiong, wanda yana cikin jagororin ya wallafa a Facebook cewa su 16 suka tattauna da rundunar yan sandan Najeriya kan zanga zangar.

Sakon 'yan sanda ga jagororin zanga zanga

Sufeton yan sanda, IGP Kayode Egbetokun ya umurci jagororin zanga zangar da su hada kai da kwamishinonin yan sanda a jihohi.

IGP Kayode Egbetokun ya ce hadin kan zai taimaka wajen kawo fahimtar juna a tsakaninsu da kuma tabbatar da zanga zangar ta gudana lafiya.

Kara karanta wannan

An gaida matasa: Muhimman nasarori 3 da barazanar zanga zanga ta samar ga talakawa

'Yan sanda za su hana zanga zanga?

Haka zalika sufeton yan sandan ya bayyana cewa zanga zangar lumana na cikin hakkin yan kasa wanda ba za su hana al'umma ba.

Sai dai ya ce hakkinsu ne su tabbatar da cewa an samu zaman lafiya a lokacin zanga zangar saboda haka ya jaddada muhimmancin bin doka da oda a lokacin zanga zangar.

Zanga zanga: Jigon APC ya tura sako

A wani rahoton, kun ji cewa jagororin jam'iyyar APC na kara daukan zafi kan shirin matasan Najeriya na yin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a dukkan jihohi.

Jigon APC a yankin kudu maso kudu, Dakta Blessing Agbomhere ya yi kira na musamman ga matasan Najeriya kan hakura da zanga zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng