Gwamnatin Tarayya Ta Kara Alawus Din 'Yan NYSC Zuwa N77,000? An Gano Gaskiya

Gwamnatin Tarayya Ta Kara Alawus Din 'Yan NYSC Zuwa N77,000? An Gano Gaskiya

  • Rahotannin da aka yaɗa a yanar gizo sun yi iƙirarin cewa gwamnatin Najeriya ta ƙara alawus ɗin da take ba masu bautar ƙasa
  • Wannan iƙirarin ya fito ne bayan gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago sun amince da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000
  • Ta hanyar amfani da wata manhaja da ake sanya ido kan yadda ake yaɗa bayanan ƙarya, Legit.ng ta binciki iƙirarin tare da bayyana sakamakon da ta samu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rahotanni sun bayyana a yanar gizo cewa gwamnatin Najeriya ta ƙara alawus ɗin da take ba masu bautar ƙasa (NYSC).

Ƴan Najeriya da suka kammala digiri na farko ko suka samu shaidar HND da suke ƙasa da shekara 30 doka ta ba su damar shiga shirin bautar ƙasa (NYSC) na shekara ɗaya.

Kara karanta wannan

"Tinubu ba masihirici ba ne": Minista ya fadi abin da ya dace 'yan Najeriya su yi

Ba a yiwa 'yan NYSC karin alawus ba
Bincike ya nuna ba a yiwa 'yan NYSC karin alawus ba zuwa N77,000 Hoto: @officialnyscng
Asali: Twitter

Ana biyan 'Yan NYSC N33, 000 a wata

Yanzu haka gwamnati tana biyan ƴan NYSC alawus na N30,000 duk wata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba a farkon watan Yulin 2024 ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Najeriya.

A ranar Litinin, 29 ga watan Yuli, Shugaba Tinubu ya rattaɓa hannu kan sabuwar dokar mafi ƙarancin albashin.

Bayan yin ƙarin albashin, an fara yaɗa jita-jita musamman a tsakanin ƴan NYSC cewa za a riƙa biyansu aƙalla N70,000 duk wata a matsayin alawus ɗinsu.

Gaskiyar batun yi wa ƴan NYSC ƙarin alawus

Duba da yadda aka yi ta yaɗa jita-jitar saboda ƴan Najeriya da dama sun yi tsammanin za a ƙara alawus ɗin ƴan NYSC bayan an yi ƙarin albashin, Legit.ng ta gudanar da bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

An maka bankin CBN kara a gaban kotu kan manyan laifuka 3, bayanai sun fito

Bayan binciken da ta gudanar, Legit.ng ta gano cewa babu wata hujjar cewa an yi ƙarin har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton saboda gwamnatin tarayya da hukumar NYSC ba su fitar da sanarwa kan hakan ba.

A zantawa da wasu da suka kammala bautar kasa a watan da ake ciki, sun tabbatarwa Legit cewa albashin N33, 000 aka biya su ba N70, 000 ba.

Haka kuma, ta hanyar yin amfani da manhajar MyAIFactChecker, wacce aka samar domin yaƙi da yaɗa labaran ƙarya a Afirika, Legit.ng ta gano cewa babu wata sahihiyar kafar yaɗa labarai da ta rahoto yin ƙarin kuɗin alawus na ƴan NYSC.

NYSC ta soke tsarin CDS

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar NYSC ta dage shirin tantancewa da yiwa al'umma hidima na wata-wata (CDS) ga ƴan bautar ƙasa saboda shirin gudanar da zanga-zanga a fadin ƙasar nan.

A ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta ne matasa suka shirya gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da kuma matsalar tattalin arziƙi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng