Gwamna Ya Yi Nasara a Kotu da Ta Ba Shi Damar Binciken Tsohon Gwamnan Jiharsa
- Yayin da ake cigaba da shari'a tsakanin Gwamna Alia Hyacinth da Samuel Ortom, kotu ta yi zama kan matsalarsu tare da yanke hukunci
- Babbar Kotun jihar da ke birnin Makurdi ta yi fatali da korafe-korafen Ortom da ke kalubalantar Hyacinth kan bincikensa
- Hakan na zuwa ne bayan Hyacinth ya kafa kwamitin binciken gwamnatin da ta shude game da zargin badakala a watan Faburairun 2024
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue - Babbar kotun jiha da ke Makurdi a jihar Benue ta yi zama kan korafin tsohon gwamna, Samuel Ortom.
Kotun ta yi fatali da korafe-korafen Ortom guda biyu inda yake neman a dakatar da gwamnatin jihar daga cigaba da tuhumarsa.
Ortom ya shigar da korafi kan tuhumarsa
Premium Times ta tattaro cewa gwamnan jihar Benue, Alia Hyacinth ya kaddamar da kwamitin binciken gwamantin da ta shude.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan rashin gamsuwa da kaddamar da binciken, Ortom ya shigar da korafi inda ya ke tuhumar kwamishinan shari'a a jihar.
Sauran wadanda ya ke kara sun hada da gwamnatin jihar da mambobin kwamitin inda ya ke tuhumarsu kan rashin kwarewa wurin binciken gwamnatinsa.
Benue: Matakin da alkalin kotun ya ɗauka
Alkalin kotun, Mai Shari'a, Tertsea Asue shi ya yanke hukuncin a yau Talata 30 ga watan Yulin 2024, cewar Punch.
Asue ya yi fatali da korafin lauyan Ortom, Maduabuchi Uba da ke neman karin lokaci kan tuhumar da ake masa.
Alkalin ya ce Orotm ya gaza cika ka'idojin kotun wurin neman tafiya a gaban kotun kafin shigar da kara a gabanta.
Ya ce Gwamna Alia ya kafa kwamitin a watan Faburairun 2024 yayin da Orotm ya shigar da korafi a watan Mayun 2024 wanda ya zarta lokacin.
Alia Hyacinth zai tona asirin manyan mutane
Kun ji cewa Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue ya sha alwashin bankada shirin masu daukar nauyin ta'addanci a jihar
Hyacinth ya ce akwai wadansu a birnin Abuja da sauran manyan ƴan siyasa da suke da hannu dumu-dumu a cikin matsalar tsaro.
Asali: Legit.ng