'Yan Bindiga Sun Shiga Wurin Ibada, Sun Sace Babbar 'Yar Siyasa
- Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace wata babbar ƴar siyasa a cikin cocinta da ke Asaba, babban birnin jihar Delta
- Ƴan bindigan sun sace Joan Mrapkpor wacce tsohuwar ƴar majalisar wakilai ce kuma ta taɓa riƙe muƙamin kwamishina a jihar
- Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa ta rasa jami'inta ɗaya a yayin harin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Delta - Wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da wata babbar ƴar siyasa kuma tsohuwar kwamishina a jihar Delta, Joan Mrapkpor wacce aka fi sani da 'Ada Anioma'.
Joan Mrapkpor, wacce tsohuwar ƴar majalisar wakilai ta tarayya ce, an yi garkuwa da ita ne a cikin cocinta lokacin da take gudanar da ibadah.
Yadda ƴan bindiga suka sace ƴar siyasar
Jaridar Leadership ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a cikin cocin da ke a kusa da gidan watsa labarai na Delta (DBS), a birnin Asaba, babban birnin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ganau ya bayyana cewa an yi hatsaniya a cikin cocin wacce ke a kusa da hedkwatar ƴan sanda, da ke kan titin DBS.
"Duk mun ranta ana kare saboda harbe-harben da aka riƙa yi. Lamarin bai daɗe da faruwa ba. An hallaka mai taimaka mata mutum ɗaya yayin da wani jami'i ya suma."
- Wani ganau
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Tashar Channels tv ta ce kakakin rundunar ƴan sandan jihar Delta, SP Bright Edafe, ya tabbatar da sace ƴar siyasar tare da mutanen da suka rasu.
Da yake magana dangane da lamarin, kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa an hallaka jami'in ɗan sanda ɗaya a yayin harin.
SP Bright Edafe ya ƙara da cewa ƴan sanda sun bi sahun ƴan bindigan kuma zai ci gaba da ba da bayanai kan lamarin nan gaba kaɗan.
Ƴan bindiga sun farmaki ƴan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun hallaka jami'an ƴan sanda mutum huɗu a jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar Litinin, 29 ga watan Yulin 2024 a kan hanyar Owerri-Onitsha a birnin Owerri, babban birnin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng