'Yan Daban Legas Sun Marawa Gwamnati Baya, Sun Yi Barazana ga Masu Shirin Zanga Zanga

'Yan Daban Legas Sun Marawa Gwamnati Baya, Sun Yi Barazana ga Masu Shirin Zanga Zanga

  • A lokacin da shirye-shirye su ka kankama kan fita zanga-zanga a sassan Najeriya, 'yan daba sun shiga batun da karfinsu
  • Wasu 'yan daba a Legas su na gangami, sannan sun ja kunnen jama'a da kar su fita zanga-zangar adawa da manufofin Bola Tinubu
  • An ji yan dabar su na gargadi 'yan kasuwa a Legas da su kuka da kansu tare da gujewa gudanar da zanga-zanga a fadin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Legas - 'Yan banga a jihar Legas sun fara gargadin mazauna jihar da su rufawa kansu asiri kar su fita zanga-zanga.

Fusatattun yan kasar nan za su fara gudanarwa da zanga-zangar lumana daga ranar Alhamis 1 - 10 Agusta, 2024 domin jaddada bukatar gyara tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan

Kungiyar duniya ta goyi bayan 'yan zanga zanga a Najeriya, ta taso 'Yan majalisa a gaba

Zanga-zanga
'Yan daba sun gargadi masu shirin zanga-zanga Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa an jiyo matasan 'yan daba ta cikin wani bidiyo su na jan kunnen 'yan kasuwar jihar da su shiga hankalinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan daba na fargaba illar zanga-zanga

'Yan daba a Legas sun yi fargabar zanga-zangar lumana da ake shirin yi za ta kai ga asarar rayuka, kamar yadda Nairaland ta wallafa. Yan bangar sun yi gargadi tare da barazana ga jama'a a kan fita zanga-zangar lumana saboda matsin tattalin arziki, tare da cewa kowa ya zauna a gida.

"Ku kadai ne ke jin yunwa? Duk wanda ya kuskura ya fito zanga-zanga, za mu yi maganinsa."

- Yan daba sun gargadi mazauna Legas

Talakawan Najeriya sun ce sun gaji da yunwa, rashin tsaro, hauhawar farashi da sauran matsaloli, saboda haka za su yi zanga-zangar kwanaki 10 domin nuna fushinsu.

Kara karanta wannan

Matasa sun zama kishiyoyin 'yan zanga zanga, sun yi tattakin goyon bayan Tinubu

Yan sanda za su kare masu zanga-zanga

A wani labarin kuma kun ji cewa rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana shirinta na samar da tsaron rayuka da dukiyoyin masu shirin zanga-zanga a fadin jihar.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an zauna da dukkannin shugabannin hukumomin tsaro kan batun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.