Ohanaeze: Dalilin da Ya Sa Matasan Ibo Ba Za Su Shiga Zanga Zangar Yunwa Ba
- Matasan Ibo sun yanke shawarar ficewa daga cikin shirin zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a farkon watan Agusta
- Kungiyar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo ce ta sanar da hakan bayan ganawa da matasan kan matsalolin shiyyar Kudu maso Gabas
- Shugaban matasan Hausawa mazauna Enugu, Aliyu Adamu Kwankwaso ya shaidawa Legit Hausa matsayarsu kan zanga-zangar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Enugu - Kungiyar raya kabilar Ibo, Ohanaeze Ndigbo ta ce matasan Ibo ba za su shiga zanga-zangar yunwa da ake shirin yi daga 1 zuwa 10 ga Agusta ba.
Kungiyar Ohanaeze ta yi magana ne da 'yan jarida a Enugu a ranar Litinin bayan taron gaggawa na kungiyar matasan Ibo mai taken "Halin da kasa ke ciki."
Jaridar The Punch ta ruwaito Ohanaeze ta ce tabbas shiyyar Kudu maso Gabas na da dalilan shiga wannan zanga-zangar, amma ba za su shiga ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ohanaeze ta magantu kan zanga-zanga
Dalilan shiga zanga-zangar da kungiyar ta zayyana sun hada da matsin tattali, rashin aikin yi, rashin shugabanci mai kyau a shiyyar.
Da yake karanta matsayar kungiyar, shugaban Ohanaeze, Chukwuma Okpalaezeukwu, ya ce matasan Ibo za su kauracewa zanga-zangar kamar yadda iyayensu suka yi.
Chukwuma Okpalaezeukwu ya ce maimakon wannan zanga-zangar, matasan za su zauna da gwamnati domin tattaunawa tare da shawo kan matsalolin da suka ambata.
Dalilin Ibo na kauracewa zanga-zanga
Bayan tattaunawa da matasan yankin, kungiyar ta yanke shawarar tattaunawa da gwamnatin tarayya da gwamnonin Kudu maso Gabas domin nemo hanyoyin magance matsalolin shiyyar.
Wannan matakin, a cewar kungiyar, zai kara karfafa alakar gwamnati da kungiyar maimakon yin fito na fito da gwamnati da ka iya haddasa rikici, inji rahoton New Telegraph.
Shugaban Ohanaeze wanda ya jaddada cewa zanga-zanga 'yanci ne na dan kasa, sai dai ya nuna fargaba cewa hakan na iya kai ga rasa rayuka, asarar dukiya kamar dai lokacin zanga-zangar EndSARS a 2022.
Matasan Hausawan Enugu sun magantu
A zantawarmu da Aliyu Adamu Kwankwaso, shugaban kungiyar matasan Hausawan jihar Enugu, ya ce su ma ba za su shiga wannan zanga-zangar ba.
A cewar Aliyu Kwankwaso, kungiyar ta fi son tattaunawa da gwamnati cikin lumana ba tare da hayaniya ba maimakon fitowa zanga-zangar nuna adawa.
Hausawan da ke zama a Enugu sun bukaci gwamnatin jihar da ma ta tarayya da su baiwa matasa damar zama a teburin sasanci domin nemo hanyoyin cigaban matasa baki daya.
'Yan sanda sun sanya dokar ta baci?
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sanda ta ce sufeta janar (IGP) Kayode Egbetokun bai bayar da umarni na sanya dokar ta baci lokacin zanga-zanga ba.
Rundunar ta ce rahoton da aka ce za a sanyawa masu zanga-zanga dokar tashi karfe 4 na yamma ba gaskiya bane, kirkirarren labari ne da aka yada domin cimma wata manufa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng