Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP ya Fadi Abin da zai Hana Tinubu Shawo kan 'Yan Zanga Zanga

Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP ya Fadi Abin da zai Hana Tinubu Shawo kan 'Yan Zanga Zanga

  • Tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba zai iya hana zanga-zanga ba
  • Tsohon shugaban ya ce Bola Tinubu ya fi kowa cin moriyar jagorantar gudanar da zanga-zanga a kasar nan
  • Uche Secondus ya ce saboda haka, shugaban ba shi da bakin da zai hana jama'a gudanar da zanga-zanga

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus ya ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba zai iya hana zanga-zanga ba.

Secondus na ganin Tinubu na gaba-gaba a cikin wadanda su ka mori yancin gudanar da zanga-zanga a kasar nan.

Kara karanta wannan

Kungiyar duniya ta goyi bayan 'yan zanga zanga a Najeriya, ta taso 'Yan majalisa a gaba

Tinubu
Uche Secondus ya ce Bola Tinubu ba zai iya hana zanga-zanga ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da hadimin tsohon shugaban a kan kafafen yada labarai, Ike Abonyi ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Zanga-zanga yancin yan kasa ce," Secondus

Kusa a babbar jam'iyyar adawa ta PDP, Uche Secondus ya ce jama'ar kasar nan su na da 'yancin gudanar da zanga-zanga, Politics Nigeria ta wallafa.

Secondus ya ce hakkin yan kasa ne su ceto kansu daga tabarbarewar tsaro da tattalin arziki, wanda gwamnatocin kasar nan su ka sabbaba.

Ya ce lalacewar harkokin kasar nan sun kai makura ne saboda jama'a sun gaza tabbatar da cewa shugabanninsu.

Secondus ya fadi yadda aka lalata kasa

Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya ce yan siyasar kasar nan sun yi amfani da addini da kabilanci wajen rarraba kan jama'a.

Ya ce saboda haka bai kamata a yi kokarin hana gudanar da zanga-zangar gama gari da aka shirya yi a mako mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

'Yan siyasa da kungiyoyi da ke goyon bayan zanga zanga da wadanda suka kushe tsarin

Zanga-zanga: Gwamnati ta nemi a dakata

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin tarayya ta shawarci 'yan kasar nan su hakura da batun zanga-zanga ganin kokarin da shugaban kasa, Bola Tinubu ke yi.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce yanzu haka an fara daukar matakan magance koken jama'a, domin an karya farashin shinkafa zuwa N40,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel