An Gaida Matasa: Muhimman Nasarori 3 da Barazanar Zanga Zanga Ta Samar ga Talakawa

An Gaida Matasa: Muhimman Nasarori 3 da Barazanar Zanga Zanga Ta Samar ga Talakawa

  • Matasan Najeriya na shirin fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a dukkan jihohin Najeriya a ranar 1 ga watan Agusta
  • Gwamnatin Bola Tinubu ta kaddamar da ayyuka masu muhimmanci domin ganin ta shawo kan matasan daga yin zanga zanga
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku muhimman nasarori uku da shirin zanga zangar ya haifar ga talakawan Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Dimbin matasa na cigaba da barazanar fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.

Shirin matasan ya sanya gwamnatin tarayya daukan matakan gaggawa da ake sa ran za su kawo saukin rayuwa a Najeriya.

Gwamnatin Tinubu
Nasarorin da shirin zanga zanga ya samar a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku muhimman abubuwan da gwamnatin tarayya ta yi da ake tunanin za su kawo saukin rayuwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Shinkafa ta dawo N40,000" Gwamnatin Tinubu ta aika sako ga masu shirin zanga zanga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Sauke farashin shinkafa a jihohi

Legit ta ruwaito cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sanar da rage farashin shinkafa da kusan kashi 50% domin saukakawa talakawan Najeriya.

Hakan na zuwa ne saboda tsadar kayan abinci na cikin manyan abubuwan da suka tilasta yan Najeriya yin zanga-zangar.

2. Fara saida danyen mai ga Dangote

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa a zaman majalisar zartarwa na jiya Litinin, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umurnin fara sayar da danyen mai ga Aliko Dangote.

Gwamnatin za ta rika sayar da mai ga Dangote ne da Naira wanda ana ganin hakan zai farfaɗo da darajar Naira da kawo saukin rayuwa.

3. Sanya hannu kan dokar karin albashi

Haka zalika, Legit ta ruwaito cewa a jiya Litinin shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar karin albashi zuwa N70,000.

Kara karanta wannan

Kungiyar duniya ta goyi bayan 'yan zanga zanga a Najeriya, ta taso 'Yan majalisa a gaba

Karin albashi na cikin abubuwan da ake tsammanin samu tun a lokacin da gwamnatin ta cire tallafin man fetur a 2023.

Masana na kallon matakan gaggawa da gwamnatin ta dauka na da alaƙa da barazanar da matasan Najeriya ke yi na shirin fara zanga zanga.

Zanga zanga: Uba Sani ya dauki mataki

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi taron gaggawa da sarakuna, malamai da jami'an tsaro domin dakile zanga zanga.

Gwamna Uba Sani ya fadi abin da ke kawo musu fargaba da ya sa suke ƙoƙarin ganin ba a yi zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ba a Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng