Zanga Zanga: Gwamnati da Jami’an Tsaro Sun Shiga Matsala, Lauya na Neman Diyyar N1bn

Zanga Zanga: Gwamnati da Jami’an Tsaro Sun Shiga Matsala, Lauya na Neman Diyyar N1bn

  • A yayin da ya rage saura 'yan kwanaki a fara zanga-zangar 'yunwa', wani lauya ya yi karar gwamnati da hukumomin tsaro
  • Lauyan, Olukoya Ogungbeje ya shigar da karar ne kan zargin gwamnati da jami'an tsaro na yunkurin dakatar da zanga-zanga
  • Daga cikin wadanda yake kara akwai gwamnatin tarayya, rundunar sojoji, 'yan sanda, SSS, DSS kuma yana neman diyyar N1bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Wani lauya mazaunin Legas, Olukoya Ogungbeje, ya shigar da karar gwamnatin tarayyar Najeriya da hukumomin tsaro inda yake neman diyyar Naira biliyan 1.

Lauyan ya shigar da karar ne bisa zargin yunkurin gwamnati da jami'an tsaro na dakatar da zanga-zangar 'yunwa' da aka shirya gudanarwa tsakanin 1 zuwa 10 ga Agusta, 2014.

Kara karanta wannan

Kungiyar duniya ta goyi bayan 'yan zanga zanga a Najeriya, ta taso 'Yan majalisa a gaba

Lauya ya yi karar gwamnati da jami'an tsaro kan zanga-zangar 'yunwa'
Masu zanga-zanga sun taru a kofar karbar harajin Lekki da ke Legas a watan Oktoban bara. Hoto: Pierre Favennec/AFP
Asali: AFP

Ana karar gwamnati, jami'an tsaro kan zanga-zanga

Rahoton Channels TV ya lissafo wadanda lauyan yake kara da suka hada da; mai ba da shawara kan harkokin tsaro (NSA) na kasa da babban hafsan tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da babban hafsan sojoji; babban sufeton ‘yan sanda (IGP); rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF); hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) da hukumar leken asiri ta kasa (SSS).

Ogungbeje ya kai karar da kansa da kuma sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa ya bayar da kudirin fara zanga-zangar lumana domin samar da shugabanci na gari a Najeriya.

Madogarar lauya wajen shigar da karar

Lauyan ya bayyana cewa karar ta dogara ne da sassa na 33, 36, 38, 39, 40 da 46 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Ya kuma bayyana cewa karar tana bin doka ta 1 da XI , ka'ida ta 1 da ta 2 na kundin ka’idojin tabbatar da hakki na 2009, jaridar New Telegraph ta ruwaito.

Kara karanta wannan

NSDC ta bankado shirin 'yan ta'adda a lokacin zanga-zanga, ta fadi matakin da ta dauka

An tsayar da 31 ga watan Yuli matsayin ranar da za a fara sauraron karar a kotu.

NSCDC ta tura jami'ai 30,000 kan zanga-zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta tura jami'anta 30,000 zuwa jihohin Najeriya domin ba da tsaro yayin da ake zanga-zanga.

NSCDC ta ce ta gano shirin 'yan ta'adda na lalata kadarorin gwamnati da kuma tayar da tarzoma, inda ta ce dole ne ta dauki matakin dakile faruwar hakan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.