Abin Boye Ya Fito: Gwamnan APC Ya Fadi Asalin Dalilin Tsoron Barkewar Zanga Zanga

Abin Boye Ya Fito: Gwamnan APC Ya Fadi Asalin Dalilin Tsoron Barkewar Zanga Zanga

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi taron gaggawa da sarakuna, malamai da jami'an tsaro domin dakile zanga zanga a Kaduna
  • Gwamna Uba Sani ya fadi abin da ke kawo musu fargaba da yasa suke ƙoƙarin ganin ba a yi zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ba
  • Matakin da gwamna ya dauka na zuwa ne a yayin matasan Najeriya ke daf da fara gudanar da zanga zanga a dukkan fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Gwamantin jihar Kaduna ta yi taro na musamman domin ganin ta shawo kan matasa masu shirin zanga zanga.

Gwamna Uba Sani ya tara sarakuna, jami'an tsaro, malaman addini, dalibai da sauran masu ruwa da tsaki domin neman mafita.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ta barke a kusa da Abuja

Uba Sani
Gwamnatin Kaduna ta yi taro kan dakile zanga zanga. Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Legit ta tattaro abin da gwamna Uba Sani ya fada ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ake tsoro a zanga zanga

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamna Uba Sani ya ce yawanci rikici na barkewa a Kaduna ne saboda zanga zanga.

Saboda haka gwamnan ya ce dole a tabbatar da cewa ba a samu barkewar zanga zanga a jihar ba domin tabbatar da kare dukiya da lafiyar al'umma.

Uba Sani: 'Ba zanga zanga ba ce mafita'

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa duk da wahalhalun da ake sha akwai bukatar neman mafita da hanyar da ba zanga zanga ba.

Gwamnan ya ce hanyoyin tattaunawa da yin taruka domin neman mafita yafi dacewa a bi maimakon zanga zanga.

Sarkin Zazzau ya yi kira ga matasa

Kara karanta wannan

Minista ya fara ganawa da matasa, Nyesom Wike zai dakile zanga zanga a Abuja

Mai martaba sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya yi kira ga matasan Najeriya kan nisantar zanga zanga.

Sarkin ya ce zanga zanga ta kawo rugujewar kasashe da dama a yankin Afrika wanda hakan ya kamata ya zama darasi ga yan Najeriya.

APC ta shirya zanga zanga a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa APC mai mulki a Najeriya ta shirya domin fara zanga zangar nuna goyon baya ga shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Sakataren kungiyar shugabannin jam'iyyar APC na jihohi, Alphonsus Ogar Eba ne ya bayyana haka a jiya Litinin a birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng