Zanga Zanga Ta Ci Sarautar Gargajiya, Wakili Ya Rasa Rawaninsa Saboda Goyon Bayan Matasa

Zanga Zanga Ta Ci Sarautar Gargajiya, Wakili Ya Rasa Rawaninsa Saboda Goyon Bayan Matasa

  • Matashi da ya goyi bayan zanga-zanga a Najeriya ya rasa rawaninsa na Wakililin matasa a Bosso da ke jihar Niger
  • Hakimin Bosso, Alhaji Mu'azu Adamu shi ya raba matashin mai suna Abdullahi Isah da sarautar shugaban matasan
  • Hakan bai rasa nasaba da shirin zanga-zanga da ake yi a fadin kasar saboda halin kunci da ake ciki da tsadar rayuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - Wani mai rike da sarautar gargajiya ya rasa rawaninsa a jihar Niger saboda nuna goyon baya ga zanga-zanga.

Hakimin Bosso da ke masarautar Minna a jihar, Alhaji Mu'azu Adama Laka ya kwace sarautar Abdullahi Isah na Wakilin matasan Bosso.

Kara karanta wannan

Fargabar zanga zanga: Tinubu ya yi wa matasa gata, ana sa ran su fasa hawa tituna

An tube matashi daga sarauta saboda goyon bayan zanga-zanga
An raba matashi da sarautar Wakilin matasa a Niger saboda goyon bayan zanga-zanga. Hoto: Bloggem3, @GRVlagos.
Asali: Facebook

Niger: Matashi ya rasa sarauta saboda zanga-zanga

Daily Trust ta tattaro cewa hakimin ya gargadi Abdullahi Isha kan cigaba da kiran kansa Wakilin matasan Bosso a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata takarda da hakimin ya rubuta a ranar 28 ga watan Yulin 2024 an tube rawanin matashin kan zargin goyon bayan zanga-zanga, cewar Daily Nigerian.

"Ina mai sanar da kai cewa an sallame ka daga mukamin Wakilin matasan Bosso nan take daga ranar 28 ga watan Yulin 2024."
"Daga yanzu bai kamata ka cigaba da kiran kanka a matsayin shugaban matasan Bosso ba."

- Sanarwar hakimin Bosso

Niger: Basarake ya yi gargadi kan zanga-zanga

Duk da basaraken bai bayyana dalilin tube matashin a wasikar ba amma hakan bai rasa nasaba da nuna goyon baya kan shirin zanga-zanga.

A cikin wata hira da ya yi, basaraken ya tabbatar da cewa an dauki mataki kan matashin ne saboda goyon bayan zanga-zanga.

Kara karanta wannan

'Yan siyasa da kungiyoyi da ke goyon bayan zanga zanga da wadanda suka kushe tsarin

Mu'azu Adamu ya ce masarautarsa ba za ta goyi bayan duk wani lamari da zai kawo tashin hankali ba da tayar da tarzoma.

Cire tallafi: Sheikh Dokoro ya shawarci Tinubu

Kun ji cewa Malamin Musulunci a Gombe, Sheikh Muhammad Adamu Dokoro ya yi magana bayan ziyarar malamai ga Bola Tinubu a Abuja.

Malamin ya ce babu bukatar su zo da ba da hakuri ko kuma tsare-tsaren shugaban wadanda an riga an san su, kuma sun wahalar da mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.