Baraka Ta Bullo: Dan Majalisar NNPP Ya Barranta da Abba kan Masarautu, Jam’iyya Ta Yi Martani

Baraka Ta Bullo: Dan Majalisar NNPP Ya Barranta da Abba kan Masarautu, Jam’iyya Ta Yi Martani

  • Jami'yyar NNPP ta yi martani bayan maganar da dan majalisarta ya yi kan rusa masarautu da rage darajarsu da Abba Kabir Yusuf ya yi
  • Shugaban jam'iyyar NNPP a jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya yi martani ga dan majalisa mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure
  • Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurum ne ya yi korafi kan rage darajar masarautun jihar da aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Jami'yyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta yi martani kan abin da ɗan majalisarta ya fada kan rage darajar masarautu.

Dan majalisar tarayya, Kabiru Alhassan Rurum ya soki gwamnatin Abba Kabir Yusuf bisa rage darajar masarautar Rano.

Kara karanta wannan

Rai baƙon duniya: Majalisar Dattawa ta sanar da mutuwar fitaccen sanatan APC

Abba Kabir Yusuf
NNPP ta yi martani ga dan majalisa kan rusa masarautu. Hoto: Abba Kabir Yusuf|Masarautar Kano
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban jam'iyyar NNPP a jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya yi martanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Korafin ɗan majalisar NNPP kan rusa masarautu

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure ya ce bai amince da rusa masarautun da Abba Kabir Yusuf ya yi ba.

Kabiru Alhassan Rurum ya kara da cewa bai amince da rage darajar masarautar Rano da Abba Kabir Yusuf ya yi ba zuwa daraja ta biyu.

Rusa masarautun Kano: Martanin NNPP

Shugaban jam'iyyar NNPP a jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce dama kowa yana da yancin fadin albarkacin baki a dimokuraɗiyyance.

Saboda haka Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce ba za su yi kokarin canza ra'ayin dan majalisar ba.

NNPP ta ce babu rikicin gida a Kano

Shugaban jam'iyyar NNPP, Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce maganar da dan majalisar ya yi ba ta nuna cewa akwai rikicin jami'yya a jihar.

Kara karanta wannan

Yusuf Gagdi: Abubuwan sani dangane da dan majalisar da ya siyawa 'yarsa motar kusan N100m

Ya ce ɗan majalisar ya fadi abin da ke cikin zuciyarsa ne kawai kuma hakan ba zai kawo sabani a tsakaninsu ba.

Masarautun Kano: Lauya ya yi magana

A wani rahoton, kun ji cewa wani lauya mazaunin Kano, Umar Sa'ad Hassan ya bayyana matsayarsa kan kirkirar masarautu uku masu daraja ta biyu.

Lauyan ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan wannan mataki inda ya ce abin a yaba ne kuma zai kawo ci gaba matuka a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng