'Yan Sanda Sun Saɓawa Gwamna a Arewa, Sun Faɗi Gaskiya Kan Fara Zanga Zanga
- Rundunar yan sandan jihar Neja ta tabbatar da cewa wasu matasa sun fito kan tituna ɗauke da kwalaye a titin zuwa Kaduna
- Hakan dai ya saɓawa gwamnatin Muhammad Umar Bago, wanda ta musanta rahoton ɓarkewar zanga-zanga a ranar Litinin
- Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Wasi'u Abiodun ya ce matasan sun fito kan tituna amma ƴan sanda suka kore su cikin lumana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Neja ta tabbatar da cewa wasu matasa sun fito kan tituna zanga-zanga da sanyin safiyar ranar Litinin.
Legit Hausa ta kawo maku rahoton yadda wasu matasa ɗauke da kwalaye suka ɓarke da zanga-zanga a yankin Suleja a kan titin Kaduna zuwa Abuja.
Wasu daga cikin rubutun da aka yi a kwalayen sun haɗa da, "Ya isa haka," "A soke tsare-tsaren cutar da jama'a," "mu ba bayi ba ne a kasar mu," da sauransu, The Cable ta rahoto wannan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Neja ta musanta zanga-zangar
A rahoton Daily Trust, mai ba Gwamna Umar Bago shawara kan harkokin yaɗa labarai, Aisha Wakaso, ta ce sam ba a yi zanga zanga ba a jihar Neja.
Gwamnatin jihar Neja ta musanta rahoton da wasu kafafen watsa labarai suka walllafa cewa zanga zanga ta ɓalle a titin Kaduna-Abuja a cikin jihar Neja.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce jami’an ‘yan sanda ne suka tarwatsa masu zanga-zangar.
Ƴan sanda sun mayar da martani
SP Abiodun ya ce:
"Wasu matasa sun fito kan titin Kaduna a Suleja sun yi ƙoƙarin toshe hanya amma kwamandan ƴan sanda na Suleja ya jagoranci jami'ai suka kore su cikin ruwan sanyi."
"Duk da haka ƴan sanda karƙashin kwamandan Suleja sun ci gaba da sintiri da sanya ido domin kai ɗauki duk wurin da ya kamata idan bukatar hakan ta taso."
Abiodun ya ce Kwamishinan ‘yan sanda ya bayar da umarnin tura ƴan sanda da kayan aiki tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro domin dakile duk wani yunƙurin karya doka da oda a Neja.
Zanga-zanga: Majalisa ta kira zaman gaggawa
Ku na da labarin Sanata Godswill Akpabio ya katse hutun majalisar dattawa, ya kira taron gaggawa kan muhimmin batun da ya shafi ƙasa baki ɗaya.
Magatakardar majalisar dattawa, Chinedu Akubueze ne ya bayyana haka a wata sanarwar da ya aike wa sanatoci ranar Litinin, 29 ga watan Yuli 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng