Hukumar NCC Ta Yi Magana Kan Layukan da Aka Rufe, Ta Ba MTN, Airtel da Sauransu Umarni
- Hukumar NCC ta yi magana kan layukan mutane da kamfanonin sadarwa suka rufe saboda rashin sanya lambar NIN
- NCC a cikin wata sanarwa da ta fitar dangane da lamarin ta umarci kamfanonin sadarwan da su buɗe layukan da suka rufe
- Har ila yau, hukumar ta kuma ja kunnen mutanen da ba su sanya lambar NIN a layukansu ba da su gaggauta yin hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci kamfanonin sadarwa da su buɗe layukan da aka rufe saboda rashin sanya lambar NIN.
Hakan na zuwa ne dai bayan a cikin ƙarshen makon da ya gabata, kamfanonin sun rufe layuka waɗanda ba a sanya musu lambar NIN ba.
Lamarin ya shafi ƴan Najeriya da dama inda suka kasa yin amfani da layukansu domin yin harkokin gabansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me NCC ta ce kan rufe layuka?
Sai dai, a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun daraktan hulɗa da jama’a na hukumar NCC, Reuben Muoka, wacce shugaban hukumar Dr. Aminu Maida, ya sanya a shafinsa na X, hukumar ta yi umarni da a sake buɗe layukan.
Hukumar ta bayyana cewa jin dadin kwastomomi shi ne abin da ta fi ba da fifiko a kai, kuma lokacin da aka bayar ya yi kaɗan jama'a su kammala sanya lambobinsu na NIN a layukansu.
"Kwastomomi su ne abin da muka fi ba fifiko, duba da wahalhalun da rufe layukan ya jawo, hukumar na umartar dukkanin kamfanonin sadarwa da su buɗe dukkanin layukan da aka rufe a ƙarshen mako."
"Kwastomomi su sani cewa sake buɗe layukan na ɗan wani lokaci ne domin a ba su damar sanya NIN a layukansu yadda ya kamata."
- Reuben Muoka
Hukumar ta kuma yi kira ga mutanen da ba su sanya lambar NIN a layukansu ba, da su gaggauta su yi hakan domin samun damar ci gaba da amfani da layukansu.
Yadda za a buɗe layin MTN
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samo hanya mai sauƙi da za a bi domin buɗe layin MTN da aka rufe saboda rashin sanya lambar NIN.
Kamfanin na MTN da sauran kamfanonin sadarwa a Najeriya sun kulle layukan miliyoyin ƴan Najeriya waɗanda ba su sanya lambar NIN a layukansu ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng