Majalisar Dattawa Ta Katse Hutu, Ta Kira zaman Gaggawa Kan Muhimmin Batun Ƙasa

Majalisar Dattawa Ta Katse Hutu, Ta Kira zaman Gaggawa Kan Muhimmin Batun Ƙasa

  • Sanata Godswill Akpabio ya katse hutun majalisar dattawa, ya kira taron gaggawa kan muhimmin batun da ya shafi ƙasa baki ɗaya
  • Magatakardar majalisar dattawa, Chinedu Akubueze ne ya bayyana haka a wata sanarwar da ya aike wa sanatoci ranar Litinin, 29 ga watan Yuli
  • Taron zai gudana ne ranar Laraba, 31 ga watan Yuli, 2024 kwana ɗaya tal gabanin ranar fara zanga-zangar adawa da tsare-tsaren Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya kira taron gaggawa na majalisar kan muhimmin batu da ya shafi ƙasa.

Magatakardan majalisar dattawan, Chinedu Akubueze ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 29 ga watan Yuli, 2024.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga taron FEC a Aso Villa kwanaki 3 gabanin fara zanga zanga

Sanata Godswill Akpabio.
Majalisar Dattawa ta kira taron gaggawa kan muhimmin batu Hoto: Godswill Akpabio
Asali: Facebook

Channels tv ta tattaro cewa sanarwar da magatakardan ya fitar ta bayyana cewa Sanata Akpabio ya kira taron ne kan, "muhimmin batun kasa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a gudanar da taron ne a ranar Laraba 31 ga Yuli, 2024, kwana daya kacal gabanin fara zanga-zangar adawa da yunwa da tsadar rayuwa a fadin kasar nan.

Meyasa Akpabio ya kira zaman majalisa?

Takardar ta ce:

“Ya ku masu girma sanatoci, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Obot Akpabio, GCON, ya ba da umarnin a kira taron gaggawa na majalisar ranar Laraba, 31 ga watan Yuli da ƙarfe 12:00 na rana.
"Ana bukatar sanatoci su yi duk shirye-shiryen da suka dace domin halartar taron domin za a tattauna batutuwan da suka shafi kasa ne baki daya."
"Ba mu ji daɗin katse wannan hutu da sanatoci ke ciki ba, mun gode da fahimtar ku."

Kara karanta wannan

Rai baƙon duniya: Majalisar Dattawa ta sanar da mutuwar fitaccen sanatan APC

Majalisa ta katse hutun watanni 2

Idan ba ku manta ba majalisar dattawa ta tafi hutun makonni bakwai wanda bisa jadawali za ta dawo daga hutun a ranar 17 ga watan Satumba, 2024.

Duka majalisu biyu - majalisar dattawa da wakilai sun tafi wannan hutu na makonni bakwai wanda shi ne hutunsu na shekara shekara, The Nation ta ruwaito.

Tinubu ya rattaɓa hannu a dokar albashi

A wani rahoton kuma Bola Tinubu ya sa hannu a dokar sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000 a fadar shugaban ƙasa a Abuja ranar Litinin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke faɗi tashin yadda za ta daƙile zanga-zangar da matasa suka shirya yi a Agusta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262