An Tona Yadda Boko Haram Ke Shirin Shiga Zanga Zanga, An Kawowa Matasa Mafita

An Tona Yadda Boko Haram Ke Shirin Shiga Zanga Zanga, An Kawowa Matasa Mafita

  • Yayin da matasa ke shirin fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya, yan sanda sun tura muhimmin sako a Yobe
  • Rundunar yan sandan jihar Yobe ta sanar da samun bayanan sirri kan yadda Boko Haram ke kokarin shiga cikin matasan
  • Yan sanda sun yi kira ga matasan da su yi taka tsantsan kan yadda za su tabbatar ba a samu shigowar bata gari cikinsu ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe - Rundunar yan sanda a jihar Yobe ta fitar da sanarwa yayin da ake shirin fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Rundunar yan sanda ta nuna cewa akwai yan ta'addar Boko Haram da ke shirin shigowa cikin matasan.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Peter Obi ya barranta da Kwankwaso, ya fadi masu daukar nauyinta

Yan sanda
Yan sanda sun yi gargadi kan zanga zanga a Yobe. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kakakin yan sanda a jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim ne ya bayyana lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda: 'Ba mu hana zanga zanga ba'

Kwamishinan yan sanda a jihar Yobe, CP Garba Ahmed ya ce ba su hana matasa fitowa zanga zanga ba a jihar.

The Guardian ta ruwaito cewa CP Garba Ahmed ya ce yin zanga zangar lumana na cikin hakkin yan kasa da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

Boko Haram: Yan sanda sun yi gargadi

Sai dai rundunar yan sandan jihar Yobe ta ce dole matasan su yi kaffa-kaffa ka da Boko Haram su shigo cikinsu a lokacin zanga zangar.

CP Garba Ahmed ya ce sun samu bayanan sirri kan waɗanda suke son shiga zanga zangar su lalata dukiyoyin al'umma.

Akwai bukatar tsarin zanga zanga a Yobe

Kara karanta wannan

Shirin zanga zanga a Kano: 'Yan sanda sun mika bukatunsu ga matasa

Rundunar yan sanda ta ce domin kaucewa shigar bata gari akwai bukatar a fitar da tsari domin yin zanga-zangar.

CP Garba Ahmed ya ce akwai bukatar matasan su bayyana wuraren da za su taru da kuma inda za su zagaya yayin zanga zangar.

An fara zanga zanga a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suka fito daga jihar Neja na nuni da cewa matasa sun fara gudanar da zanga-zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Masu zanga zangar sun fito kan tituna ne dauke ta alluna suna rera wakokin da kira ga gwamnatin tarayya kan kawo saukin rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng