Borno: Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan Boko Haram a Wani Samame

Borno: Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan Boko Haram a Wani Samame

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi abin a zo a gani bayan sun sheƙe ƴan ta'addan Boko Haram a wani samame a jihar Borno a Arewa maso Gabas
  • Sojojin na bataliya ta 151 da ke aiki a rundunar Operation Hadin Kai sun hallaka ƴan ta'adda takwas yankin Bula Marwa da ke jihar
  • A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ƙara da cewa sojojin sun yi nasarar ƙwato makamai tare da wasu kayayyaki daga hannun ƴan ta'addan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

Dakarun na bataliya ta 151 na rundunar Operation Hadin Kai sun kashe ƴan ta'adda takwas a yankin Bula Marwa da ke dab da ƙauyen Siraja a jihar Borno.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa daga Arewa sun ba mutanen yankinsu muhimmiyar shawara kan zanga-zanga

Sojoji sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram a Borno
Sojoji sun sheke 'yan ta'addan Boko Haram a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Yadda sojoji suka hallaka ƴan ta'adda

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta fitar a ranar Talata, 29 ga watan Yulin 2024, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce ƴan ta’addan sun gamu da ajalinsu ne a ranar 28 ga watan Yulin 2024 a yayin wani samame da sojojin suka kai a maɓoyarsu, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Dakarun sojojin sun kuma ƙwato abin harba gurneti, bindiga ƙirar MK da wata jaka mai ɗauke da kayan ƴan ta'addan.

Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun sojojin na ci gaba da bincike a yankin domin zaƙulo ragowar ƴan ta'addan da ke wajen.

Rundunar sojojin ta bayar da tabbacin cewa jami'anta za su ci gaba da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin ci gaba da kare lafiya da dukiyoyin jama'a da kawo ƙarshen ayyukan ta'addanci.

Kara karanta wannan

Matasa na shirin zanga zanga, jami'an tsaro sun harbe ƴan fashi har lahira

Karanta wasu labaran kan sojoji

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram a dajin Sambisa na jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram mutum shida a maɓoƴarsu da ke cikin dajin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng