Baraka ta Shiga Kungiyar Yarbawa a kan Zanga Zangar Adawa da Manufofin Tinubu

Baraka ta Shiga Kungiyar Yarbawa a kan Zanga Zangar Adawa da Manufofin Tinubu

  • Ana ci gaba da samun rabuwar kai tsakanin 'yan Najeriya a kan batun zanga-zanga da ake shirin gudanarwa a kasar nan
  • An samu rabuwar kai tsakanin kungiyar Yarbawa ta Afenifere da aka samu tsagin Ayo Adebanjo yana goyon bayan zanga-zangar
  • Daya bangaren na Reuben Fasoranti ya barranta kansa da zanga-zanga, inda ya ke ganin ba za a samu alherin komai daga hakan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsagin Reuben Fasoranti na kungiyar dattawan yarbawa ta Afenifere ta barranta kanta da zanga-zangar da 'yan kasar nan ke shirin farawa.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Peter Obi ya barranta da Kwankwaso, ya fadi masu daukar nauyinta

Wannan na zuwa bayan wani tsagi na kungiyar karkashin Ayo Adebanjo ta bayyana goyon bayanta a kan zanga-zangar kwanaki 10 da ake shirin yi.

Bola Tinubu
Kan Afenifere ya fara rabuwa a kan zanga-zanga Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta tattaro cewa sakataren kungiyar Afenifere na kasa, Abagun Kole Omololu ya ce zanga-zangar ba za ta haifar da da mai ido a kasa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: Afenifere ta goyi bayan Tinubu

Kungiyar yarbawa ta Afenifere ta bayyana cewa da gaske akwai yunwa a kasa, amma shugaban kasa Bola Tinubu ya na kokarin magance ta da sauran matsaloli.

Sakataren kungiyar na kasa tsagin Fasoranti, Abagun Kole Omololu ya ce ba zai kyautu a gudanar da zanga-zanga a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin kawo gyara ba.

Ya ce matsalar ba Najeriya ce kadai ke cikin halin matsi ba, an samu matsalar tattalin arziki a kasashen duniya masu tarin yawa, Naija News ta wallafa.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri: Ministan Tinubu ya ba 'yan Arewa shawari kan zanga-zangar da ake shirin yi

"Yan kasa na da 'yancin zanga-zanga," Afenifere

Kungiyar kare hakkin yarbawa ta Afenifere ta ce 'yancin kowanne dan Najeriya ne ya fito zanga-zangar lumana idan akwai bukatar haka.

Amma kungiyar na ganin zanga-zangar da aka shirya gudanarwa daga 1-10 Agusta, 2024 na dauke da mummunar manufa da zai kawo hargitsi.

Minista ya fara tattaunawa kan hana zanga-zanga

A wani labarin kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya fara tattaunawa da matasa domin dakile yunkurin gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ta bayyana cewa yanzu ba lokaci ba ne da 'yan kasa za su gudanar da zanga-zanga ganin cewa Bola Tinubu ya na kokari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.